Ana fama da karancin ma’aikata a Asibitin kwararru na Bauchi
Sabon Shugaban Asibitin kwararru na Jihar Bauchi Dokta Zailani Isa ya ce suna fama da karancin ma’aikata a asibitin inda ya yi kira ga Gwamnan Jihar Barista Mohammed Abubakar ya kara dauka musu sababbin ma’aikata a asibitin don su gudanar da aikinsu yadda ya kamata. Dokta Zailani Isa ya bayyana haka ne lokacin da suke […]
Sabon Shugaban Asibitin kwararru na Jihar Bauchi Dokta Zailani Isa ya ce suna fama da karancin ma’aikata a asibitin inda ya yi kira ga Gwamnan Jihar Barista Mohammed Abubakar ya kara dauka musu sababbin ma’aikata a asibitin don su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Dokta Zailani Isa ya bayyana haka ne lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu a ofishinsa a garin Bauchi, inda ya ce akwai gadajen kwanciya 400 a asibitin da ma’aikatan jinya 400 da kwararrun likitoci mutum 30, kuma likitoci 23 daga cikinsu ma’aikata ne na dindindin, yayin da sauran sukan zo ne jefi-jefi.
“Muna kira ga Mai girma Gwamna Abubakar cewa akwai wasu daga cikin mutanen Jihar Bauchi da aka tura su kasashen waje domin karatun likita muna fatar idan suka dawo zai turo mana su wannan asibiti domin yin aiki ga al’ummar jihar,” inji shugaban.
Sai ya gode wa Gwamna Abubakar kan tura musu man dizal tirela daya don amfani da shi a janaretocin asibitin, a duk lokacin da aka dauke wutar lantarki daga layin wuta na kasa.
Tsohon Gwamnan Jihar Malam Isa Yuguda ne ya bude a asibitin wanda aka gina a harabar Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Abubajar Tatari Ali da ke kofar Ran a garin Bauhci a karshen wa’adin mulkinsa bayan ya gina shi, sakamakon mika tsohon Asibitin kwararru don mayar da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa balewa.