Mahaifi ya tsere bayan jikkata kananan ’ya’yansa

’Yan sanda suna farautar wani magidanci da yawa ’ya’yansa ’yan makarantar firamare duka tare da ji musu munanan ruanuka.

Mahaifi ya tsere bayan jikkata kananan ’ya’yansa

‘Yan Sandan Najeriya

’Yan sanda suna farautar wani magidanci bayan da ya lakada wa ’yarsa mai shekera 11 da wanta dan shekara 11 da duka tare da ji musu munanan ruanuka.

Wakilinmu a Legas ya ruwaito cewa malamar makarantar yarinyar ce ta kai kara bayan da ta ga dalibar tata da munanan raunuka a sassan jikinta.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce hedimastar makarantar da ke yankin Orile Agege ta kai kara ofishin ’yan sanda bayan dalibar ta tababtar mata da cewa mahaifinsu, wanda ya saba dukansu ne ya yi mata hakan.

“Yarinyar mai shekaru 11 ta shaida wa malamar ajinsu cewa mahaifinta ne ya lakada musu duka ita da wanta mai shekaru 13.

“Amma yanzu an kwace yaran ana ba su kulawa da duba lafiyarsu, sannan an damka su a hannun wata yarsu ta ci gaba da kula da su.

“Amma wanda ake zargin ya tsere daga gidan kafin zuwan ’yan sanda,” a cewar Hundeyin.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa