Ana fargabar ɓarkewar Sanƙarau a Sakkwato
An buƙaci mazauna da su gaggauta kai rahoton duk wata alama ta rashin lafiya zuwa mahukunta mafi kusa.

Gwamnan Jihar Sakkwato Ahmad Aliyu
An gargaɗi mazauna da su kwana cikin shirin daƙile yaɗuwa cutar Sanƙarau a yayin da cututtuka masu alaƙa da ita suka soma bayyana a wasu ƙananan hukumomin Jihar Sakkwato.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Faruk Umar Wurno ne ya yi wannan gargaɗi haɗi da bayar da shawarar a wani jawabi da ya fitar a ranar Talata.
Kwamishinan ya yi bayanin cewa ya zama wajibi duk wasu alamomi da aka gani a ɗauka a shiga da su ɗakin gwaje-gwaje a bincika domin a tabbatar ko ƙoshin lafiyar al’umma.
Dakta Faruk Umar ya ce ma’aikatarsa za ta saka ido kan jami’an lafiya na gwamnati da masu zaman kansu domin a tabbatar an daƙile yaɗuwar cutar.
Ya gargaɗi mazauna cewa a koyaushe su kasance a ankare wurin ɗaukar matakin kariya ga cututtuka na yau da kullum.
Ya buƙaci jama’a su riƙa gaggauta sanar da jami’an kiwon lafiya mafi kusa da zarar sun ga wata alama ta rashin lafiya kamar zazzaɓi ko ciwon kai mai tsanani.
Kwamishinan ya nanata muhimmancin tabbatar da tsaftar jiki da muhalli sannan jama’a su yi iya ƙoƙari wajen kaucewa shiga cunkoso da zama a wurin da iska ta wadata.
Ya buƙaci jama’a da su kai rahoton duk wata alama ta cuta ko wata rashin lafiya da ba a saba da ita ba a asibiti mafi kusa.
A kwanakin dai zafi yana tsananta a wasu jihohin ƙasar ciki har da Sakkwato, lamarin da babu shakka yana da nasaba da haddasa yaɗuwar cutar ta Sanƙarau.