Ana fargabar kai harin ’yan bindiga a makarantun Bayelsa

Hakan dai da ya tilasta wa shugabannin makarantu kulle makarantun.

Ana fargabar kai harin ’yan bindiga a makarantun Bayelsa

An shiga yanayi na zaman ɗar-ɗar da fargaba a makarantu daban-daban da ke faɗin Jihar Bayelsa a ranar Juma’a, biyo bayan wata jita-jita na bogi game da shirin kai hari da ’yan bindiga za su yi.

Hakan dai da ya tilasta wa shugabannin makarantu kulle makarantun.

Daily Trust ta gano cewa fargabar ta samo asali ne daga wani saƙo da wani mai amfani da kafar Facebook mai suna Sen Promise Etete JP ya wallafa, inda ya yi iƙirarin cewa, ’Yan sa-kai sun kama ’yan fashin daji, kuma suna neman kuɗin fansa har Naira miliyan 50 a kan kowane a Jihar Bayelsa,” lamarin da ya nuna cewa ‘yan bindigar za su iya kai harin ɗaukar masauki.

Iyayen yara da masu riƙo yara sun yi dafifi zuwa makarantu, musamman makarantun da ke yankunan Gbarain da Polaku a Yenagoa, babban birnin jihar domin kwashe ’ya’yansu.

Lamarin ya kuma tilasta wa makarantu da dama a faɗin jihar kulle kofofinsu domin kauce wa afkuwar kowane irin garkuwa da ɗalibai.

Idan za a iya tunawa, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, malamai da ɗaliban makaranta sun gudanar da zanga-zanga a ranar Litinin domin nuna ɓacin ransu kan sace yaran makaranta a jihar Oyo, inda suka buƙaci a sake su ba tare da sharaɗi ba.

Da yake magana a kan lamarin, wani malami kuma mai magana da yawun ƙungiyar Matasan Polaku, Kwamared Ebiweni Chris Kenigua ya bayyana cewa jita-jitar cewa an sace ɗalibai daga makarantu ƙarya ne.

Ya ce: “A halin yanzu muna makaranta muna rubuta jarabawar WAEC ta darasin Geography, kodayake jita-jitar ya kawo cikas ga harkokin karatu domin iyaye sai tururuwa suke yi suna kwashe ’ya’yansu.

Masarautar Polaku da Gbarain sun kasance yankuna mafi zaman lafiya da tsari. Zaman lafiya kaɗai muke buƙata, kada ku haddasa tashin hankalin da bai zama dole ba a unguwanninmu.” In ji shi.