Ana fuskantar karancin abinci a Nijar
Kimanin mutum miliyan biyu da dubu 100 ne suke fuskantar matsalar karancin abinci a bana, a Jamhuriyyar Nijar.Hukumar Agajin Gaggawa ta Majalisar dinkin Duniya ce ta bayyana hakan, a wani rahoton da ta fitar game da sha’anin agaji a Nijar .Sai dai ba wannan ne karon farko da kasar ke fuskantar matsalar karancin abinci ba, […]
Kimanin mutum miliyan biyu da dubu 100 ne suke fuskantar matsalar karancin abinci a bana, a Jamhuriyyar Nijar.
Hukumar Agajin Gaggawa ta Majalisar dinkin Duniya ce ta bayyana hakan, a wani rahoton da ta fitar game da sha’anin agaji a Nijar .
Sai dai ba wannan ne karon farko da kasar ke fuskantar matsalar karancin abinci ba, kamar yadda shugaban kungiyar kare hakkin gajiyayyu a kasar, Malam Sidi Fodi Hamidou ya bayyana.
A wani labarin kuma, wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun kai hari a garin Yebi a yankin Bosso na jihar Diffa a jumhuriyar Nijar, inda suka kashe mutane tara.
Hakazalika wasu mutanen fiye da 10 sun jikkata.
Hukumomin Jihar Diffa dai wadanda suka tabbatar da lamarin sun ce, wannan shi ne hari na biyu da aka kai a garin a kasa da makwanni biyu, duk da kusancinsa da Bosso, inda ke da sansanin sojoji.