Ana Gasar gemu ta duniya
A watan Nuwamban kowace shekara mazaje da dama kan nuna kwarewa wajen iya ajiye gemu da gashin baki a gasar ajiye gemu ta duniya da ake gudanarwa shekara-shekara. A bana an gudanar da gasar ce a birnin Leifenden-Echterdigan da ke kasar Jamus inda mutane da dama suka nuna irin salonsu na ajiye gemun a wani […]
A watan Nuwamban kowace shekara mazaje da dama kan nuna kwarewa wajen iya ajiye gemu da gashin baki a gasar ajiye gemu ta duniya da ake gudanarwa shekara-shekara. A bana an gudanar da gasar ce a birnin Leifenden-Echterdigan da ke kasar Jamus inda mutane da dama suka nuna irin salonsu na ajiye gemun a wani bangare na “Nuwamba” wanda wani kokari ne na wayar da kai da batutuwan da suka shafi lafiyar maza.
Gidajen talabijin da dama ciki har da shirin NBC’s Today sun nuna gasar a shirye-shiryensu, inda ya bayyana cewa kimanin maza 300 ne daga sassan duniya suka shiga gasar ta bana. Ga wasu daga cikin ’yan takarar nan mun kawo muku hotunansu don kashe kwarkwatar ido.