Ana hantarar mu da sunan ’yan bindiga a Kurmi — ’Yan Arewa

Sarkin Samarin ya shawarci ’yan Arewa masu zuwa cirani Kudu maso Yamma da su yi taka-tsantsan kuma su guji yin abin da zai iya haifar da zargi a kansu.

Ana hantarar mu da sunan ’yan bindiga a Kurmi — ’Yan Arewa

Wasu ’yan Arewa da ke zaune a jihohin Kudu maso Yamma sun koka bisa abin da suka kira ƙaruwar cin zarafi da kuma nuna masu wariya, a yayin da ake fuskantar matsalolin tsaro a wasu sassan yankin.

A zantawarsa da Amimiya, Alhaji Ahmad S. Salihu, Sarkin Samarin Ile-Ife a Jihar Osun kuma Shugaban Ƙungiyar Tallafa wa Ci-gaban ’Yan Arewa, reshen Jihar Osun, ya ce ’yan Arewa a Kudu maso Yamma suna fuskantar ƙalubale da ke ƙaruwa saboda fargabar rashin tsaro.

Ya ce sace ɗalibai da malamai tare da garkuwa da aka yi da su kwanan nan a Jihar Oyo ya ƙara ta’azzara tashin hankali a faɗin yankin, lamarin da ya haifar da ƙaruwar sa ido da sintiri a tsakanin mazauna yankin, amma kuma yana haifar da cin zarafin mutane musamman ’yan Arewa da ba su ji ba, ba su gani ba.

“A ranar Alhamis ɗin da ta gabata, wata ƙungiyar ’yan banga a Ile-Ife ta ceto wasu matasa ’yan Arewa su shida daga yunƙurin kisan gillar da aka yi shirin yi musu. Matasan sun taso ne daga Arewa zuwa Jihar Osun a cikin wata babbar mota ɗauke da shanu, tumaki da awaki.

An sauke su a garin Ibodi, wani yanki kusa da Ilesa mai yawan jama’a ’yan Arewa da ke harkokin kasuwancinsu a yankin a nan Jihar Osun, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa Ife-Wara a Ƙaramar Hukumar Ilesa ta Yamma, inda a nan ma akwai tarin al’ummar Hausawa,” in ji shi.

Sarkin Samarin ya bayyana cewa bayan sun shafe kwanaki da dama a kan babbar motar da ta ɗauko su daga Arewa zuwa Kudu, matasan sun kasance cikin datti da ƙura, kuma wasunsu sun tara gashi irin na dada ko rasta ya cika da ɓƙura da datti.

“Maimakon da babbar motar ta sauke su, su je nemi gidan wanka su yi wanka su sauya kaya kafin su nufi inda za su je, sai suka hau babura na acaɓa suka nufi Ile-Ife.

Wasu matasan Yarbawa sun tare su a hanya, ganin kamanninsu da jakunkunan da suke ɗauke da su, sai suka yanke hukuncin cewa ’yan bindiga ne kuma za su kashe su,” in ji shi.

Ahmad S. Salihu ya yaba wa ’yan banga na yankin da suka hana a ɗauki doka a hannu kan matasan.

“Daman can muna aiki tare da ƙungiyar ’yan bangan da ke aiki a nan Ile-Ife. Da suka ga abin da ke faruwa, sai suka shiga tsakani suka hana a kashe matasan, nan take suka tuntubi Sarkin Hausawan Ile-Ife, wanda shi ma ya sanar da ni muka isa wajen.

“Bayan mun je inda ake tsare da matasan, muka yi musu tambayoyi. Mun gano cewa ba ’yan bindiga ba ne, matafiya ne da suka taso daga Arewa, waɗanda suka shafe kwanaki suna a kan motar shanu, wanda hakan ya sauya kamanninsu.

“Nan take aka ba mu su, muka tuntuɓi shugabannin al’ummar Arewa a garin da suka nufa kuma muka sanya su a hanyar zuwa garin. Ba don shiga tsakani da ’yan bangar suka yi ba, da an kashe waɗannan matafiya su shida,” in ji shi.

Sarkin Samarin ya shawarci ’yan Arewa masu zuwa cirani Kudu maso Yamma da su yi taka-tsantsan kuma su guji yin abin da zai iya haifar da zargi a kansu.

“Ya kamata su guji tafiya a saman manyan motocin dakon dabbobi, kuma su guji ayyukan farauta ba tare da wani dalili ba ko wani abu da zai iya sa mutane su yi tunanin su masu laifi ne,” in ji shi.

Haka kuma, a ranar Lahadin da ta gabata, a garin Ile-Ife da ke jihar Osun, Sarkin Samarin Ile-Ife, Alhaji Ahmed S. Salihu, ya karɓi wasu matafiya 11, ciki har da mata da yara ƙanana, waɗanda aka tsare a yankin Madoke na jihar Osun.

 

Ya ce an yi zargin cewa matafiyan ‘yan bindiga ne, har ma wasu suka yi ƙoƙarin kai musu hari, amma ‘yan banga suka sanar da Sarkin Hausawan Ile-Ife, wanda daga nan ya aike shi zuwa wurin domin bincike.

 

“Da na isa wurin na yi musu tambayoyi, sai na gano cewa matafiya ne daga jihar Zamfara. Suna tafiya tare da wani babban rago da kuma baburan acaɓa guda biyu, kuma hanyarsu ta nufi garin Madoke da ke nan jihar Osun,” in ji shi.

 

Ya ce bayan tabbatar da cewa matafiya ne ba ‘yan bindiga ba, sai suka garzaya da su zuwa fadar babban basaraken Yarbawa na yankin Madoke, wanda shi ma ya tabbatar da cewa ba ‘yan bindiga ba ne, matafiya ne daga jihar Zamfara.

 

“Na yi wa basaraken bayani cewa abin da na gano shi ne matafiya ne ba ‘yan bindiga ba. Nan take aka ba ni takardar yarjejeniya (undertaking) ɗauke da sunayensu, na sanya hannu na karɓe su. Basaraken ya yaba mana, sannan ya yi wa waɗanda suka kamo su nasiha, inda ya ce idan aka ga irin wannan lamari kada a ɗauki doka a hannu, sai a sanar da mahukunta. Ya kuma ce tunda sun riga sun iso lafiya, ya kamata a yi taka-tsantsan, tare da yin kira da a daina irin wannan tafiya ba tare da tsari ba,” in ji Sarkin Samarin.

 

Sarkin Samarin ya shaida wa Aminiya cewa matafiyan sun haɗa da wata tsohuwa guda ɗaya, mata matasa uku da kuma samari maza.

 

“Sun zo ne a cikin wata mota mai ɗaukar kaya, ba motar shanu ba. Abin da ya sa aka yi zargin su da kasancewa ‘yan bindiga shi ne yadda kura da datti suka rufe su, kasancewar sun yi tafiya a saman motar ɗaukar kaya tare da jakunkunansu, babura biyu da kuma rago guda ɗaya. Haka kuma wasu daga cikin samarin sun tara irin gashin da ake dangantawa da ‘yan bindiga. Saboda haka, ina kira ga ‘yan Arewa masu son yin irin wannan tafiya da su yi taka-tsantsan,” in ji shi.

 

Ya ƙara da cewa a halin yanzu Sarkin Hausawan Ile-Ife, Alhaji Salisu Usaini, tare da shi Sarkin Samarin, suna shiga gidajen rediyo a jihar Osun domin wayar da kan jama’a tare da yi musu ƙarin haske kan yadda za a kauce wa irin waɗannan matsaloli.

 

Yadda ake tsangwamarmu a Ekiti — Fulani

Hakazalika, wani shugaban al’ummar Fulani a Jihar Ekiti, Malam Zayyanu Muhammad, ya ce mazauna jihar da suka haɗar da Fulani da Hausawa suna fuskantar babban ƙalubale, saboda matsalolin tsaro a sassan Jihar Kwara da maƙwabtanta.

“Wannan yana haifar da yawan kama mutanenmu ba tare da wani dalili ba, musamman matafiya. Ana kama mutane da yawa, ana cin zarafinsu kuma ana wulaƙanta su a kowace rana.

“Masu kula da harkokin noma, da jami’an Amotekun da sauran jami’an tsaro na jihohi suna cin zarafin mutanen da ke kiwon dabbobi musamman ma Fulani. Lamarin yana ƙara zama abin damuwa yayin da lokacin zaɓe ke gabatowa,” in ji shi.