Ana horar da ’yan Boko Haram a kasata – Shugaban Somaliya
Shugaban kasar Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud ya ce ’yan Boko Haram da ke yakar Najeriya suna samun horo a kasarsa.Shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya bayyana haka ne a kasar Jamus a ranar Lahadi a wajen wani taro kan tsaro.Shugaba Mohamud ya ce kungiyoyin ’yan ta’adda da ke kasashen Afirka suna da alaka da juna don […]
Shugaban kasar Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud ya ce ’yan Boko Haram da ke yakar Najeriya suna samun horo a kasarsa.
Shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya bayyana haka ne a kasar Jamus a ranar Lahadi a wajen wani taro kan tsaro.
Shugaba Mohamud ya ce kungiyoyin ’yan ta’adda da ke kasashen Afirka suna da alaka da juna don haka akwai bukatar kasashen Afirka su hada hannu domin murkushe barazanarsu.
“Idan Somaliya ba ta zaune lafiya, daukacin yankin kahon Afirka zai ci gaba da fuskantar barazana, kuma lamarin zai shafi daukacin Nahiyar Afirka. Akwai shaidu da hujjojin da suka tabbatar da cewa a wasu lokuta an horar da ’yan Boko Haram a Somaliya kuma sun koma Najeriya.”
Ya kara da cewa: “Wadannan ’yan ta’adda suna ta’allake da juna, kungiyoyin da suke a tsare don haka ya zama wabiji mu ma mu kasance a tsare.”
kasar Somaliya tana fama da hare-haren mayakan al-Shabab da almundahana da kuma fadace-fadacen siyasa.
Al-Shabab wadda ake alkanta ta da kungiyar al-kaeda, ta rika kai hare-hare ga jami’an gwamnati da fararen hula, tare da tsallaka zuwa kasar Kenya.
Takwararta ta Boko Haram wadda ta yi mubaya’a ga kungiyar IS da ke tafka ta’asa a Syria da Irak a watan Maris din bara, ta kashe fiye da mutum 126 a cikin watan Janairun da ya gabata kadai. Kuma ta ci gaba da kai miyagun hare-hare a watan Fabrairun da muke ciki, inda harin da ta kai a sansanin ’yan gudun hijira a farkon wannan wata ya hallaka fiye da mutum 58. Boko Haram ta kashe fiye da mutum dubu 20 tare da tilasta fiye da miliyan biyu da dubu 600 yi gudun hijira daga garuruwansu.