Ana iya rigakafin cutar yoyon fitsiri – Dokta Nasiru

Me yake haifar da cutar yoyon fitsari?Babban abin da yake haifar da wannan ciwo shi ne wasu matan kugunsu ba ya da karfi, ma’ana wajen da da yake zama. Shi ne daga bisani sai su kamu da wannan cuta. Wata kuma wajen da dan yake zama ya yi karami saboda haka idan ta haihu sai […]

Ana iya rigakafin cutar yoyon fitsiri – Dokta Nasiru
Ana iya rigakafin cutar yoyon fitsiri – Dokta Nasiru

Me yake haifar da cutar yoyon fitsari?
Babban abin da yake haifar da wannan ciwo shi ne wasu matan kugunsu ba ya da karfi, ma’ana wajen da da yake zama. Shi ne daga bisani sai su kamu da wannan cuta. Wata kuma wajen da dan yake zama ya yi karami saboda haka idan ta haihu sai ta kamu da cutar yoyon fitsari, wasu kuma suna doguwar nakuda. Wani lokacin idan ba a samu kwararren likita ba, sai ya yanka mace a wurin da bai kamata ba a lokacin haihuwa. Cutar daji na mafitsara ma wasu lokutan tana haifar da cutar yoyon fitsari a tsakanin mata wannan shi ne abin da zan fada. Bayan haka duk matan da ta kamu da wannan cuta bayan muna ba ta magani kyauta sannan abinci ma kyauta ne muke ba ta a asibitin. Tun lokacin da aka ba ni shugabancin wannan asibiti ina da alaka mai kyau tsakanina da hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya da masarautar Ningi saboda haka muna mutakar godiya bisa irin goyon bayan da suke ba mu. Gwamnatin Jihar Bauchi tana taimaka mana daidai gwargwado.
Wani hali wannan asibiti yake ciki?
Asibitin Yoyon Fitsiri na garin Ningi, shi ne kadai a wannan shiyya na Arewa maso Gabas, kuma yana ba da magunguna ne kyauta ga matan da suka kamu da cutar yoyon fitsari. Wannan asibiti na Gwamnatin Tarayya ne kuma an kafa asibitin ne domin tallafa wa masu cutar yoyon fitsari da sauran cututtukn da suka shafi mata. Kuma duk da cewa asibitin yana Ningi akwai dimbin mutane da suke amfana da shi. Babu wasu matsaloli da muke fuskanta a halin yanzu domin muna da likitoci masu yawa kuma Gwamnatin Tarayya tana ba mu kayan aiki daga lokaci zuwa lokaci. Kuma akwai matan da suke zuwa daga jihohin Borno da Yobe da Adamawa da Gombe da Taraba da Jihar Bauchi, kuma mafi yawan marasa lafiyan sun kamu ne da cutar yoyon fitsarin.
Cutar yoyon fitsari yana karuwa ne ko raguwa a Arewa maso Gabas?
Maganar gaskiya cutar yoyon fitsari a tsakanin mata tana karuwa a shiyyar Arewa maso Gabas domin duk lokacin da muka nemi wadanda za mu yi musu tiyata kyauta sai mun samu dimbin mata masu cutar. Bayan haka wayar da kan al’umma da muke yi daga lokaci zuwa lokaci ta kafafen watsa labarai shi ma ya taimaka sosai wajen wayar da kan mutanen karkara wasu lokutan za mu iya cewa cutar tana raguwa a wasu sassa.
Wadanne matsaloli kuke fuskanta a asibitin?
Abin da zan fada shi ne Gwamnatin Tarayya a karkashin Shugaban kasa Muhammadu Buhari tana da manufofi masu kyau game da wannan asibiti, amma ana fama da matsalar kwararrun ma’aikata. Na biyu kuma asibitin bai dade ba domin gwamnatin Jihar Bauchi ce ta ba da wajen da aka gina. Babban abin da muke bukata shi ne ba mu da wasu gine-gine masu yawa a cikin asibitin muna fata Gwamnatin Tarayya za ta kawo mana dauki. Kasafin kudi na bana gwamnati ta ware mana wasu kudi domin gudanar da wasu dimbin ayyuka. Jinyar wannan cuta tana bukatar kwararren likita da ma’aikatan jinya, gaskiya muna fama da karancin ma’aikata domin ba kowa ne zai iya wannan aiki na cutar yoyon fitsari ba. Matsalar kayan aiki, alhamdullahi Gwamnatin Tarayya tana ba mu kudin sayen kayan aiki kuma akwai kungiyoyin da suke ba da gudunmawa kan kiwon lafiya muna da alaka mai kyau tsakaninmu da su.

Mene ne sakonka ga ma’aikatan asibitin da sauran ’yan Najeriya?
Babban sakona ga daukacin ma’aikatan wannan asibiti shi ne kowa ya kula da aikinsa, sannan su ci gaba da tausaya wa marasa lafiya domin kowa da tunaninsa, dole wasu lokutan su fuskanci kananan matsaloli daga wajen marasa lafiya. Tun lokacin da aka bude wannan asibiti babu wani koke da muka samu daga wajen marasa lafiya ko wani ma’aikaci ya musguna musu. Ina tabbatar maka idan muka samu likita ko ma’aikacinmu yana musguna wa marasa lafiya tabbas za mu dauki mataki mai tsauri a kansa. Ga ’yan Najeriya kuma su fahimci cewa ana rigakafin cutar yoyon fitsari don haka a daina kyamar masu cutar, duk wadda ta kamu da cutar a yi saurin kai ta asibiti a kan lokaci. Duk matar da ta kamu da cutar kyauta ake ba da maganin ba a karban ko kwabo, wannan shi ne abin da zan fada a takaice.