Ana kama Akawun karamar Hukumar Kazaure kan zambatar maigadi
Jami’an tsaro na farin kaya Sibil Defens sun kama Mataimakin Akawun karamar Hukumar Kazaure bisa zarginsa da cin bashin Naira dubu 85 a banki ta amfani da sunan wani maigadi ba tare da sanin maigadin ba. Kwamandan Hukumar NSDSC na Jihar Jigawa Alhaji Gidado Fari ya sanar da manema labarai haka a Dutse, inda ya […]
Jami’an tsaro na farin kaya Sibil Defens sun kama Mataimakin Akawun karamar Hukumar Kazaure bisa zarginsa da cin bashin Naira dubu 85 a banki ta amfani da sunan wani maigadi ba tare da sanin maigadin ba.
Kwamandan Hukumar NSDSC na Jihar Jigawa Alhaji Gidado Fari ya sanar da manema labarai haka a Dutse, inda ya ce Mataimakin Akawun mai suna Malam Bello Halliru ya rubata takardar neman rancen Naira dubu 80 da 500 da sunan maigadin ya kuma amshi kudin a banki inda ake yanke wa maigadin kudi daga cikin albashinsa alhalin bai amshi bashi ba.
Tuni aka gurfanar da akawun a gaban Kotun Majistare ta Kazaure inda Mai shari’a Mustapha Abba ya bayar da umarnin a tura akawun gidan maza domin bai wa ’yan sanda damar kammala bincike a kan wanda ake tuhumar.
Maigadin mai suna Malam Ibrahim muhammed Galadanci wanda mazaunin Kazaure ne ya sanar da jami’an bankin halin da yake ciki saboda duk wata sai an yanke masa kudi daga albashinsa lamarin da ma’aikatan bankin suka shaida masa cewa ai ya amshi bashi kuma ga wanda ya yi masa garanto na amsar da bashin.
Aminiya ta samu labarin cewa da bincike ya yi bincke ne sai aka gayyaci Mataimakin Akawun domin ya amsa tanbayoyi, daga bisani ne ma’aikakatan bankin suka gano cewa shi ya aikata wannan zamba domin cutar da maigadin, lamarin da ya sa aka sanar da jami’an tsaron na farin kaya wato Sibil Defens, suka kama shi suka mika shi gaban kotu.
Malam Gidado ya ce wanda ake tuhumar yana gidan maza, inda su kuma suke ci gaba da bincike domin gano ya yi wa wasu mutane irin waccan zamba a karamar Hukumar Kazaure, inda nan da zuwa mako biyu za a sake mayar da shi gaban kotu domin ci gaba da sauraron shari’arsa.