An kama ma’aurata sun shirya wa jaririn da suka sace biki
Sun sace jaririn washegarin haihuwarsa, suka shirya masa biki.
An kama wasu ma’aurata a Kano bayan sun shirya kasaitaccen biki wa wani jariri saboda haihuwa da suka sato washegarin haihuwarsa a asibiti.
Bikin da ma’auratan suka yi na samun da namji a gidansu da ke unguwar Rijiyar Zaki ya sanya tababa a zukatan makwabta, saboda sun san cewa matar ba ta dauke da juna biyu, don haka suka tsegunta wa hukuma.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce dubun ma’auratan ta cika ne bayan wani magidanci mai suna Rabi’u Muhammad, mazaunin unguwar Gayawa, ya kawo musu kara cewa an dauke daya daga cikin tagwayen da aka haifa masa.
“Matarsa ta haifi da tagwayen ne a Asibitin Koyarwa na Abdullahi Wase a ranar 7 ga Satumba, 2021, inda aka kwantar da ita.
“Barci ne ya dauke ’yar uwar matarsa tasa da ke kula da jariran a zauren shiga dakin masu jego; Da ta farka sai ba ta ga daya daga cikin jariran ba,” inji Kiyawa.
Ya ce bayan samun rahoton ne Rundunar ta tura jami’anta masu binciken kwakwaf karkarshin jagorancin SP Daniel Itse Amah su gano inda jaririn yake, su dawo da shi, sannan su kamo wadanda suka sace shi.
“Jami’an sun je an rufe asibitin, suka bincike ko’ina, amma ba a ga jaririn ba.
“Da aka ci gaba da bincike da tattara bayanai, sai aka kama wata mata mai shekara 22 da mijinta mai shekara 50 a unugwar Rijiyar Zaki, wadanda aka kwato jaririn a gidansu,” a cewarsa.
Ya ce a lokacin da aka fara bincikar ma’auratan, matar ta amsa cewa ita ce ta sace jaririn a Asibitin Koyarwa na Abdullahi Wase bayan mijinta ya hure mata kunne saboda yadda ya dade yana neman da namiji.
A cewarsa, an mika jaririn ga mahaifansa, amma Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya umarci Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar su ci gaba da bincikar ma’aurantan, idan suka gama sai a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya.