Ana kara yin gine – gine a bakin Kogin Kaduna
Wadansu mutane na kara yin gine-gine a bakin Kogin Kaduna inda wadansu suke gina gidaje don kasaita yayin da wasu ke yi don neman matsuguni duk da ambhaliyar ruwa da ke mamaye su da damina a ’yan shekarun nan.Gina gidajen har wa yau ana jin na da alaka da bunkasar da garin Kaduna yake yi, […]
Wadansu mutane na kara yin gine-gine a bakin Kogin Kaduna inda wadansu suke gina gidaje don kasaita yayin da wasu ke yi don neman matsuguni duk da ambhaliyar ruwa da ke mamaye su da damina a ’yan shekarun nan.
Gina gidajen har wa yau ana jin na da alaka da bunkasar da garin Kaduna yake yi, sakamakon tudadowar jama’a daga yankunan karkara zuwa birane ko saboda guje wa kuncin zaman gidajen haya.
A shekarun baya dai ambaliyar ruwa ta mamaye gidaje da dama da ke gabar Kogin Kaduna da suka hada da garuruwan Rigachikun da Rafin Guza da Unguwar Dosa da Malali da Unguwar Rimi da Kabala da Kakuri da Tudun Wada da Nasarawa da Kudenda da sauransu.
Akwai gidajen da aka gina a bakin Kogin Kaduna a yankin Unguwan Rimi kusa da Gadar Patrick Ibrahim Yakowa a kan hanyar da ta fito daga Titin Gobarau ta nufi Kamozo ko matatan man fetur na Kaduna, wasu an kawata su ta hanyar sa na’urar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana da sauransu.
Wakilinmu ya lura mazauna wadannan gidaje musamman ma wani guda daya da ruwan ke shanye shi, yana zaune ne cikin tasku domin a kowace shekara a lokacin ruwan sama, idan ruwa ya yi ambaliya yana mamaye gidan dungurungun. A bara da ruwa ya yi ambaliya, ya rushe akasarin katangar gidan.
Rahotanni sun ce akasarin gidajen da ke gefen Kogin Kaduna sai da aka yi wa mazaunansu fito da kwale-kwale daga gidajen tun daga garin Rigachikun har zuwa yankin Rafin Guza zuwa Kudenda.
Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Hukumar Raya Birane ta Jihar Kaduna (KASUPDA) Malam Nuhu Garba ya ce sun yi ta kokarin ganin mai gidan ko mazuna gidan da ya fi kowanne fuskantar matsala a bakin kogin domin jin ta bakin su amma abin ya ci tura. Ya ce sun rubuta takarda don neman haka, amma shekara kusan biyar ke nan shiru.
Ya ce dalilin neman mai gidan shi ne su sanar masa cewa ya yi gini ne a filin hukuma kuma hadari ya yi gini a gabar kogin, domin hakan yana jefa rayukansu cikin hadari.
Malam Nuhu Garba ya kara da cewa hukumarsu tana bin tanadin doka kafin ta dirar wa irin wadannan gidaje na ’yan share-wuri-zauna.
Duk yunkurin da Aminiya ta yi don jin ta bakin mazuna gabar kogin ya ci tura.