Ana karancin filin binne gawawwaki a Gaza
Sakamakon farmakin da kasar Isra’ila take kaiwa zirin Gaza, Falasdinawa da ke kudancin garin suna fuskantar karancin filin binne mamata.Wani mazaunin yankin mai suna Abu Sada ya shaidawa tashar talabijin ta Aljazeera cewa “gawawwaki sun warwatsu akan tituna wanda yake hassada doyi mai karfi. Ya ce hare-haren Isra’ila ya shafi ko ina da kowa sakamakon […]
Sakamakon farmakin da kasar Isra’ila take kaiwa zirin Gaza, Falasdinawa da ke kudancin garin suna fuskantar karancin filin binne mamata.
Wani mazaunin yankin mai suna Abu Sada ya shaidawa tashar talabijin ta Aljazeera cewa “gawawwaki sun warwatsu akan tituna wanda yake hassada doyi mai karfi. Ya ce hare-haren Isra’ila ya shafi ko ina da kowa sakamakon haka ba mu da wajen buya.” Inji shi.
Ya ce gidajen adana gawawwakin garin Rafah ya cika makil wanda hakan ya sa dangin mamata ba su da wani zabi da ya wuce adana gawawwakin ’yan uwansu a cikin na’urar sanyaya abinci wato (firji). Abu Sada ya ci gaba da cewa “dalilin da ya sa wasu gawawwakin ba a iya masu sutura ba, shi ne ba su da wani dangi a kusa da ya rage a raye, sai na nesa sakamakon farmakin da Isra’ila take kaiwa ta sama a garin. Ta ya ya zamu binne gawawwakinmu bayan farmakin Isra’ila yana isa har cikin makabartunmu wadanda galibi cike suke saboda yawan jama’ar da suka rasa rayukansu a wannan rikicin.”
Majalisar dinkin Duniya ta ce a ranar Asabar da ta gabata mutum hudu ’yan gida daya sun hallaka bayan wani da Isra’ila ta kai wani hari ta sama a gidan da suke zaune. Ya yin da wani harin kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutum takwas suma ’yan gida daya a ranar Lahadin da ta gabata.
A halin yanzu kusan mutum 2000 ne suke rasa rayukansu da wadansu guda 9406 da suka samu raunuka tun fara farmakin Isra’ila a yankin zirin Gaza kimanin wata daya kenan. Hakazalika, akalla sojojin Isra’ila guda 63 ne suka rasa rayukansu a rikicin ciki har da fararen hula guda biyu da wani dan kasar Thailand.