Ana karancin kaji a kasuwar kaji da ke Jos

Shugaban  kasuwar kaji da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato, Alhaji Sani Abdul’Azeez ya bayyana cewa sakamakon cutar murar tsuntsaye da aka yi, a shekarar da ta gabata  yanzu suna fuskantar matsalar rashin kaji a kasuwar ‘yan kaji da ke garin Jos. Alhaji Sani Abdul’azeez ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa […]

Ana karancin kaji a kasuwar kaji da ke Jos

Shugaban  kasuwar kaji da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato, Alhaji Sani Abdul’Azeez ya bayyana cewa sakamakon cutar murar tsuntsaye da aka yi, a shekarar da ta gabata  yanzu suna fuskantar matsalar rashin kaji a kasuwar ‘yan kaji da ke garin Jos. Alhaji Sani Abdul’azeez ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya.

Ya ce mu ‘yan kasuwa masu sayar da kaji, a wannan kasuwa  muna cikin wani yanayi na tausayawa. Domin a halin yanzu ana namen kaji ido rufe, saboda bakukuwan kirsimeti da sabuwar shekara. 

Ya ce amma yanzu babu kajin saboda a baya masu gidajen kiwon kaji sun fuskanci matsalar masassarar ciwon kaji, wadda sakamakonta  kaji sun yi ta mutuwa. 

 “A da a daidai irin wannan lokaci na watan Disamba ana samun kaji ana sayarwa, har karshen watan ba tare da kajin sun yanke ba. Saboda a da kusan duk masu kiwon kaji sukan ce ba za su sayar da kajinsu ba, sai a watan Disamba. Don haka ake samun kajin a wadace. Amma a bana babu kajin’’. 

Alhaji Sani Abdul’Azeez ya yi bayanin cewa  suna samun kaji daga gidajen kajin da ake da su a jihar nan, domin akwai gidajen kaji da yawa a jihar nan. 

Ya ce amma a bana yawaicin irin wadannan gidajen kaji ba su da kajin balle su sayar musu. 

Ya ce yanzu  ‘yan kasuwar wannan kasuwa  suna kame-kame ne kawai, wajen nemo kajin da za su sayar. Don haka suke tafiya zuwa Gombe da Adamawa da Sakkwato gonakin kaji don sayo kajin. 

Ya ce suna da masu zuwa suna sayen kaji daga wurare daban-daban kamar Abuja da Fatakwal da sauran sassan kudancin kasar nan.  

Daga nan ya yi kira ga gwamnati ta tallafa wa masu gidajen kaji da suka yi asara sakamakon wannan annoba ta murar tsuntsaye, domin farfado da wannan harka. 

Har’ila yau ya yi kira ga kamfanonin abincin kaji kan su sassauta farashin kayan abincin kajin da suke yi.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50