Ana karkatar da harajin da ake tarawa a Kasuwar Dawanau
Bincike da wakilinmu ya gudanar bayan samun korafe-korafen ’yan kasuwar kayan abinci ta duniya da ke Dawanau ya gano cewa mafiya yawan kudin harajin da ake karba daga hannunsu ba sa shiga aljihun karamar Hukumar Dawakin Tofa da kasuwar ke cikinta.Mafiya yawan ’yan kasuwar da wakilinmu ya zanta da su sun ce suna biyan haraji […]
Bincike da wakilinmu ya gudanar bayan samun korafe-korafen ’yan kasuwar kayan abinci ta duniya da ke Dawanau ya gano cewa mafiya yawan kudin harajin da ake karba daga hannunsu ba sa shiga aljihun karamar Hukumar Dawakin Tofa da kasuwar ke cikinta.
Mafiya yawan ’yan kasuwar da wakilinmu ya zanta da su sun ce suna biyan haraji bisa ka’idar da aka sanya musu, amma abin takaici shi ne an kasa inganta kasuwar an bar ta cikin mawuyacin hali, duk da ficen da ta yi a Afirka ta Yamma.
Sannan sun nuna damuwa cewa faduwar damina ta sa kasuwar ta Dawanau ba ta da dadin shiga da motocin daukar kaya saboda lalacewar kusan duk hanyoyin kasuwar.
Binciken ya gano, tashar motar manyan motoci da ke kasuwar inda nan ne ofishin tattara harajin yake tana cikin wani mawuyacin hali, inda a yanzu haka ta zamo wani karamin kududdufi.
Wani direban babbar mota da ya bukaci a sakaye sunansa ya shaida wa Aminiya cewa suna mamakin irin kudin da ake karba a hannunsu amma abin haushi, tashar tana lalace babu gyara sabanin wasu kasuwanni da ba su yi girman kasuwar Dawanau ba.
Su kuwa ’yan kasuwa masu kasa kayan abinci sun ce su da kansu ne suke kokarin gyara magudanun ruwa da yin ciko a kasuwar sannan kungiyar Ci gaban Kasuwar tana kokari kwarai wajen gudanar da ayyuka a kasuwar amma karamar hukumar ba ta kula da muhimman ayyuka illa kokarin karbar haraji da ake cewa ba ya isa hannunta yadda ya kamata.
Masu korafin sun ce kudin haraji da ake karba a kasuwar za su taimaka wajen inganta ta da samar da ababen more rayuwa ga ’yan kasuwar kamar yadda ake yi a sauran kasuwanni.
Wata majiya a karamar Hukumar Dawakin Tofa ta shaida wa Aminiya cewa majalisar karamar hukumar ta kafa wani kwamiti mai karfi da zai yi bincike kan yadda ake karbar kudin shiga a kasuwar, bayan ganin tabarbarewar yanayin tara harajin, tare da nemo karin hanyoyin inganta kasuwar.