Ana kokarin janyo bore a Saudiyya – Kwamndan Askar

Shugaban Jami’an Tsaron kasar Saudiyya (Askar) Sheikh Abdullatif Al-Sheikh ya ce suna kokarin murkushe ayyukan masu tsattsauran ra’ayi a tsakanin jami’ansu. Sheikh Abdullatif Al-Sheikh ya fada wa wata jaridar Saudiyya cewa masu tsattsauran ra’ayin na kokarin janyo bore a kasar.Kalamansa na zuwa ne bayan wata doka da aka kafa a ranar Litinin da ta gabata […]

Ana kokarin janyo bore a Saudiyya – Kwamndan Askar

Saudi King Abdullah bin Abdul Aziz al-Saud attends the opening session of the annual summit of the Gulf Cooperation Council (GCC) in Muscat on December 29, 2008. Oman’s Sultan Qaboos called for establishing a mechanism to stabilise oil prices in order to overcome the global financial crisis, at the opening of the summit today. AFP […]

Shugaban Jami’an Tsaron kasar Saudiyya (Askar) Sheikh Abdullatif Al-Sheikh ya ce suna kokarin murkushe ayyukan masu tsattsauran ra’ayi a tsakanin jami’ansu.
Sheikh Abdullatif Al-Sheikh ya fada wa wata jaridar Saudiyya cewa masu tsattsauran ra’ayin na kokarin janyo bore a kasar.
Kalamansa na zuwa ne bayan wata doka da aka kafa a ranar Litinin da ta gabata wacce ta tanadi daurin kusan shekara 20 ga duk dan kasar Saudiyya da ya shiga yaki a cikin wata kasa ko kuma ya shiga cikin wata kungiya ta ’yan ta’adda.
Matasan Saudiyya da dama sun tsallaka zuwa kasar Syria don yaki a bangaren dakarun ’yan tawaye masu kishin addini da suke kokarin kawar da Shugaba Bashar Assad.
Sabuwar dokar ta ce duk dan kasar da aka gano ya shiga yakin da ake yi a Syria ko wasu kasashen zai sha daurin shekara uku zuwa shekara 20 a gidan yari.
Duk da cewa gwamnatin kasar Saudiyya tana goyon bayan wasu ’yan adawar Syria. Sai dai tana fargabar cewa ’yan kasar nata za su iya koyo tsattsauran ra’ayin addini, sannan su dawo kasar domin yi mata bore.
A watan Nuwamban bara an kai wa kasar hare-haren roka shida da aka harba daga yankunan da ke kusa da iyakar kasar da kasashen Iraki da Kuwait.
Hukumomin Saudiyyar sun ce ba su san wanda ya harba makaman ba ko kuma inda aka harbo su.
Sai dai wata karamar kungiyar gwagwarmaya ta ’yan Shi’a mai suna Dakarun Mukhtar ta dauki alhakin kai harin.
kungiyar ta ce harin gargadi ne ga Saudiyya kan ta kiyayi shiga harkokin Iraki.
A baya dai gwamnatin Iraki da ’yan Shi’a suka mamaye ta ta bayar da sammacin kama shugaban kungiyar.