Ana kokarin samar da fasahar da za ta sa masu Ciwon Siga rage kiba suna barci

Wani binciken masana ya gano akwai yiwuwar mutanen da ke fama da Ciwon Siga za su iya rage kiba lokacin da suke tsaka da sharar bacci ta hanyar amfani da sabuwar fasahar da suke kokarin tabbatarwa. Masu binciken a Jami’ar Portsmouth da ke Ingila, dai na neman wadanda za su gwada sabon tsarin na rage […]

Ana kokarin samar da fasahar da za ta sa masu Ciwon Siga rage kiba suna barci

Kwararru a dakin gwaji

Wani binciken masana ya gano akwai yiwuwar mutanen da ke fama da Ciwon Siga za su iya rage kiba lokacin da suke tsaka da sharar bacci ta hanyar amfani da sabuwar fasahar da suke kokarin tabbatarwa.

Masu binciken a Jami’ar Portsmouth da ke Ingila, dai na neman wadanda za su gwada sabon tsarin na rage kiba kansu, wanda ya kunshi  takaita shakar iska a lokutan bacci.

Abin da binciken ke son ganowa dai a yanzu shi ne ko bacci a tantuna na musamman da ke da karancin iskar Oxygen da bil-Adama ke shaka na taimaka wa jiki sarrafa Sigar da ke jini da kuma rage kiba ko a’a.

Binciken baya dai ya nuna karancin iskar Oxygen a wuri na rage wa dan-Adam karsashin cin abinci, da kona sinadaran kuzari ga mai ciwon Sigar samfurin type 2.

Don haka wadanda za a gwada binciken a kan su za su kwanta cikin tantunan na musamman da tawagar binciken za ta sanya a gidajensu na tsawon kwana 20.

A kwanaki 10 na farko dai za a sanya iskar Oxygen da ba ta haura kaso 15 ba cikin tantunan, wato kwatankwacin wacce ke cikin jirgin sama mai dauke da fasinjoji a sararin samaniya, sanye da na’urorin da za su dinga auna nauyi da kibarsu, da abincin da suke ci, da hawa ko saukar sikarin jikinsu, hadi da  samfurin bahaya da fitsarinsu.

Babban malami a jami’ar da ke Sashen Kimiyyar Wasanni da Lafiya, da motsa jiki, wato Dokta Ant Sheperd ya ce: “Da hasashen samun karin adadin masu ciwon Siga zuwa miliyan 700 nan da shekarar 2045 a duniya, ya zamo dole mu dage wajen gano hanyoyin magance ciwon, domin talaka ya samu rage kashe makuden kudi a bangaren lafiya, ya ji da abin kai wa bakin salati.”