‘Ana kora ta a gidan haya saboda nakasar ’ya’yana’

Wani magidanci a Gombe, fadar Jihar Gombe, mai suna Malam Abdullahi Ibrahim ya koka kan yadda ake korarsa daga kowane gidan haya saboda nakasar da ta samu ’ya’yansa uku da suka koma makafi kuma guragu.Malam Abdullahi Ibrahim, mazaunin Unguwar Jauro Innayo da ke bayan Kwalejin Arabiyya ta Gwamnati (ATC) a Gombe, ya ce yana da […]

‘Ana kora ta a gidan haya saboda nakasar ’ya’yana’
‘Ana kora ta a gidan haya saboda nakasar ’ya’yana’

Wani magidanci a Gombe, fadar Jihar Gombe, mai suna Malam Abdullahi Ibrahim ya koka kan yadda ake korarsa daga kowane gidan haya saboda nakasar da ta samu ’ya’yansa uku da suka koma makafi kuma guragu.
Malam Abdullahi Ibrahim, mazaunin Unguwar Jauro Innayo da ke bayan Kwalejin Arabiyya ta Gwamnati (ATC) a Gombe, ya ce yana da ’ya’ya uku maza, wadanda dukansu makafi ne kuma guragu, “Bayan haihuwarsu da ’yan watanni kadan ne, sai kansu ya daina tsayawa wuri daya, sai kuma hakiya ta kama idanunsu, kuma da suka kai wasu shekaru sai su makance, kafafunsu su shanye kuma hakan ya sa ake kora ta a gidajen da nake haya,” inji shi.
Yaran masu suna Auwalu, mai shekara 11 da Sama’ila, mai shekara takwas da kuma Umar, mai shekara biyar, a yanzu sun zama makafi kuma guragu, mahaifinsu ya ce, an haife su lafiya, kuma matarsa na zuwa awo asibiti kuma ana yi wa yaran allurar rigakafi har da na shan inna, amma da sun kai wani lokaci sai matsalar makanta da gurguntaka ta same su.
Ya ce kananan asibitoci suke zuwa saboda ba ya da karfin zuwa manya asibitoci, kuma bai taba neman taimakon jama’a kan matsalar ba balle gwamnati da sai mai hanya. “Yanzu da na ga abin ba sauki ne na nemi ’yan jarida ku taimaka min ku gaya wa duniya da gwamnati halin da nake ciki da yaran,” inji shi.
Ya ce shi karamin dan kasuwa ne mai sayar da ’yan kunne a cikin akwaku da ke fuskantar wahalar daukar dawainiyar yaran saboda lalurarsu.
Da waklinmu ya je daya daga cikin gidajen da Malam Abdullahi ya yi haya, matar da ya zauna a gidanta mai suna Hajiya Adama a Unguwar London Maidorawa ta ce ya shiga gidanta haya ne lokacin da wani dan yuniyal ya kawo shi ya biya kudin wata shida. Ta ce ba ta san halin da yaran suke ciki ba, sai da safe ta ga su ukun makafi ne kuma guragu.
Hajiya Adama ta ce ba su wuce kwana uku a gidanta ba, sai jama’a suka samu labarinsu kuma kafin ta ankara sai gidan ya zama kamar gidan kallon kwallo saboda yadda mutane manya da yara ke tururuwa zuwa kallon yaran.
Ta ce da ta fara hana shiga gidan don kallon yaran ne, sai aka koma ana jifarsu, shi ne ya sa ta ce wa Malam Abdullahi ya karbi kudinsa ya tashi daga gidan ba za ta iya zama da su ba.
A daya gidan da Malam Abdullahi ya zauna, a gaban Sakandaren Gwamnati ta Gandu, gidan wani Malam Yahaya da aka ce ya zauna na tsawon shekara takwas ta hannun wakilin maigidan, an ce wakilin na rasuwa ne da zai biya kudin haya kai-tsaye ga maigidan da ya gane yana da ’ya’ya nakasassu ya ce ba zai karbi kudinsa ba ya je ya nemi wani gidan.