Ana kula da mutum 400 kan cutar Ebola – Minista Halliru
Dokta Haliru Alhasan Minista a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ya tattauna da wakilinmu na Sakkwato kan halin da ake ciki a yanzu kan lamarin da ya shafi cutar Ebola da maganar janye yajin aiki da likitocin kasar nan suka yi: Aminiya: Wane hali ake ciki game da cutar Ebola da ta kunno kai a […]
Dokta Haliru Alhasan Minista a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ya tattauna da wakilinmu na Sakkwato kan halin da ake ciki a yanzu kan lamarin da ya shafi cutar Ebola da maganar janye yajin aiki da likitocin kasar nan suka yi:
Aminiya: Wane hali ake ciki game da cutar Ebola da ta kunno kai a Najeriya?
Dokta Haliru: A halin yanzu gaskiya mun samu nasarori kan shawo wannan matsala, kamar yadda kuka sani a Jihar Legas mutum daya ne ke kwance a sansanin da ake kulawa da masu cutar Ebola a yanzu. Duk da wani abu mai muni ya faru wato daya daga cikin wadanda ake kulawa da su da ya yi huldar farko da Patrick Sawyer dan Laberiya da ya shigo da cutar, ya sulale wa jami’an lafiya da ke kula da shi domin duba jikinsa ya tafi garin Fatakwal, inda ya samu wani abokinsa likita suka tafi ya ba shi magani, kaddara ta gitta likitan ya kamu da wannan cuta ta Ebola kuma ya rasu. Mun samu labarin ne bayan aukuwarsa ta hanyar matarsa da ta zo ta ce tana ganin alamun tana tare da wannan cutar, da aka bincika aka samu tana da ita, mijinta ne ya sanya mata, shi ko mijin ya samu sanadin cudanya da wanda ya kai dan Laberiya din asibiti ne, bayan gwajin gawar likitan da muka yi mun tabbatar yana da wannan cuta ta Ebola.
Aminiya: Ana yabon Gwamnatin Tarayya da na jihohi kan matakin da suka dauka na hana yaduwar cutar, shin hakan na nuna an farfado da sha’anin kiwon lafiya?
Dokta Haliru: Gaskiya kiwon lafiya kodayaushe yana kan gaba a shirye muke da wadannan abubuwan in suka zo mana ba zato ba tsammani. Muna da shirye-shiryen ko-takwana da na gaggawa mu dauki mataki kan lamari. Wannan shiri da muka yi na Ebola ya nuna a shirye muke mu yaki duk wata cuta in ta shigo mana.
Aminiya: A halin yanzu mutum nawa suka rasu dalilin wannan cuta, kuma mutum nawa ke fama da ita?
Dokta Haliru: Mutum 15 muka tabbatar na dauke da wannan cuta har dan Laberiyar, ’yan Najeriya 12 suka kamu da cutar a yanzu, bakwai daga cikinsu sun samu sauki an sallame su daga asibiti, shida sun rasu, akwai mutum daya dake karbar magani a Legas, sai kuma mutum biyu da ke Fatakwal. Amma muna duba mutum 400, bisa tsammani cutar za ta fito daga gare su, a halin da ake ciki ba su da cutar saboda sun yi hulda da masu cutar muke duba su. A kullum sai an auna jininsu da yanayin zafin jikinsu. Kamar yadda muka sani ita cutar tana da lokacin bayyana sai dai yanzu ta tashi daga kwana biyu zuwa mako uku in har wannan lokaci ya yi ba a ga alamunta ba, to mutum ba zai kamu da cutar ba.
Aminiya: Ina aka kwana game da likitocin kasar nan da aka kore su, kuma a yanzu suka janye yajin aiki?
Dokta Haliru: Gwamnatin Tarayya tana kokari sosai ta inganta abubuwa a kasar nan musamman a Ma’aikatar Lafiya. Mun yi zama da likitocin fiye da sau 18 kuma kowane zama sai mun kwashe sa’a 12 kan yadda za a cimma ma tsaya mai alfanu, domin tattaunawa kadai ce ke samar maslaha koda ba a samu abin da ake so dari bisa dari ba, kuma ana kan tattaunawa da su. Mu ba mu kori kowa ba, ba wani likita da Gwamnatin Tarayya ta kora, abin da kawai muka yi mun tsayar da shirinsu na horar da likitoci, domin bai kamata kana yajin aiki kuma kana aiwatar da wani shiri a bayan fage ba, shi ne gwamnati ta bukaci su dawo aiki sannan su fadi bukatunsu. Amma da suka janye yajin aiki gwamnati ta kyale su sun ci gaba aiwatar da shirinsu na horar da kananan likitoci.
Aminiya: Ko kana da wani kira da za ka yi ga jama’a?
Dokta Haliru: Kiran da zan yi ga jama’a su kwantar da hankalinsu, ita cutar Ebola Alhamdulillah mun samu nasara tsayar da ita, inda a wuri biyu ne kawai ta bayyana wato Legas da Fatakwal. Kuma hira da mai cutar ba zai yi sanadin kamuwa da ita ba, ko me cutar na tare da ku sai an samu cudanya ta jiki da jiki, don haka mutane kada su ji tsoro su je su yi lamuransu, amma su kara kula kada mutum ya tafi kasashen da aka hana tafiya irin su Senegal da Laberiya da Gini da Saliyo da sauransu. Ya kamata mutanenmu su daina shigowa da naman daji, kuma duk wanda ya ji wani yanayi da bai saba jinsa ba, to ya je asibiti. Mun dauki matakin a kan iyakokinmu ta hanyar ba da horo ga ma’aikatan kula da shige da fice, dukan jiragen samanmu manya da kanana ana binciken lafiyar mutane masu shigowa da fita da na’ura ta musamman, haka wuraren saukar da bakinmu. Kuma akwai hadin gwiwa a tsakaninmu da ma’aikatun lafiya na jihohi domin su tanadar mana wurin ajiye marasa lafiya in har ta faru, kuma duk wani matakin da ya kamata za mu rika daukarsa domin kare lafiyar mutanen kasar nan.