Ana nema wa gwaggwon biri hakki a Amurka

A wannan makon ne wata kotu a birnin New York za ta saurari karar da wani mai rajin kare hakkin dabbobi da ma mutane, mai suna Stebe Wise, inda zai bayar da hujjojin sa na cewa bai dace a rika ajiye gwaggwon biri ba a cikin keji , da ma duk wata dabba mai siffar […]

Ana nema wa gwaggwon biri hakki a Amurka
Ana nema wa gwaggwon biri hakki a Amurka

A wannan makon ne wata kotu a birnin New York za ta saurari karar da wani mai rajin kare hakkin dabbobi da ma mutane, mai suna Stebe Wise, inda zai bayar da hujjojin sa na cewa bai dace a rika ajiye gwaggwon biri ba a cikin keji , da ma duk wata dabba mai siffar mutane.

Ya ce, birai musamman gwaggwon biri bai dace ana takura musu ba, ana sanya su cikin keji, domin ko wasu abubuwa nasu tamkar na bani Adama ne, kuma hakan da ake yi musu tamkar cin zali ne.
Shi dai Stebe ba wannan ne karo na farko da ya kai wannan batun gaban kotu ba, ya yi haka a wani lokaci can baya, amma alkali bai saurare shi ba, sai a wannan karon alkalin ya ba shi damar ya bayyana gaban kotun domin kafa hujjojin sa kan abin da yasa yake ganin a bar gwaggwon biri suna yawo kamar mutane.
Stebe ya fi mayar da hankalin sa ne a kan wani gwaggwon biri da ake kira Tommy, kuma yana nan cikin birnin New York ne cikin wani babban keji. Ya ce idan anyi hakan za a bai wa wannan gwaggwon birin damar shiga cikn ’yan uwansa da ke yawon su a Florida.
Ya ce dabbobi masu nasaba da wasu abubuwan bani Adama ya dace a ba su wata damar walwala ciki ko har da barin su sake, a daina sa su cikin keji ko kuma hana su walwala.
Ya ce wannan gwagwon birin fa da yake magana a cikin kejin da aka kulle shi, har an sa masa talabijin domin ya rika kallo, amma kuma ake hana shi fita kamar sauran mutane.