Ana neman ƙwace filin masallacin ’yan Arewa don gina dandalin baɗala a Abiya
An rusa katangar da ta kewaye masallacin aka gina shaguna da rumfunan sayar da giya
Sarkin Hausawan Aba a Jihar Abiya, Alhaji Sarki Shehu Bello na II, ya roƙi attajirai Musulmi a Nijeriya su kai musu ɗauki domin sayen wani filin masallaci a garin Aba wanda wasu suke ƙoƙarin saya su mayar da shi wajen ayyukan masha’a.
Sarkin Hausawan ya buƙaci kada bari damar mallakar wurin ta suɓuce daga hannun Musulmi, domin shi kaɗai ne masallacin da ke wajen gari da baƙin Musulmi ’yan kasuwa daga Arewa da wasu ƙasashen Afirka ke amfani da shi wajen ibada a duk lokacin da suka shiga garin Aba domin kasuwanci.
Sarkin Hausawan ya ce “Shekara 38 da suka gabata ne wani ɗan ƙabilar Ibo mazaunin garin Aba mai suna Cif Orji Igwe ya bayar da hayar filin ga al’ummar Hausawa masu harkar kasuwanci a ‘Shoe Plaza’ a bayan Kasuwar Duniya ta Ariaria da ke garin Aba.
“Kafin rasuwar Cif Orji Igwe, Hausawan sun ci gaba da biyan sa kuɗin hayar filin mai girman ƙafa 50/10 har zuwa yanzu da iyalinsa suke buƙatar sayar da filin.”
Ya ce abin farin ciki, Cif Orji Igwe ya bar rubutacciyar wasiyya ga iyalinsa cewa idan sun tashi sayar da filin bayan mutuwarsa to su tabbatar cewa sun sayar ga Hausawan da suke biyan kuɗin hayar filin.
“Bayan rasuwarsa ce muka faɗa cikin matsala da wasu mutane suka bi ta bayan gida suka haɗa kai da wasu iyalin marigayi Cif Orji Igwe suka yi cinikin filin a ɓoye.
“Daga baya sun rusa katangar da ta kewaye masallacin tare da gina shaguna da rumfunan sayar da giya,” in ji shi.
Sarki Shehu Bello ya ce bayan naɗa shi Sarkin Hausawan Aba a watan Nuwamban shekarar 2021 “A lokacin ’yan Arewa da suke kasuwanci a ‘Shoe Plaza’ sun kawo kuka gare ni kan lamarin, inda hankalina ya tashi matuƙa amma sai na gudanar da binciken ƙwaƙwaf tare da bin diddigi.
“A binciken ne na gano gaskiyar abin da mutanen nawa suka faɗa.
“Kuma na yi nasarar samun kwafen rubutacciyar wasiyyar da Cif Orji Igwe ya bayar ga iyalinsa kafin ya rasu,” in ji shi.
Ya ce, “Hakan ne ya sa na fara fafutikar ƙwato wa mutanena haƙƙinsu.
“Na kai kuka ga ofisoshin manyan jami’an tsaro da dukkan masu ruwa-da-tsaki na Aba inda bayan ɗaukar tsawon lokaci muka yi nasara mahukuntan Jihar Abiya suka bayar da umarnin cewa wajibi ne a yi aiki da wasiyyar da wanda ya mallaki fili ya bari.
“Hakan ne ya kai ga tayar da cinikin filin da aka ƙulla a ɓoye.”
Sarki Shehu Bello ya ce “Yanzu haka iyalin marigayi Cif Orji Igwe sun yi wa filin masallacin kuɗi a kan Naira miliyan 200.
“Sai dai babbar matsalar da muke ciki ita ce rashin wanda zai iya sayen filin a cikin mutanena domin talakawa ne.
“Saboda haka ina roƙon attajirai Musulmi a ƙasa baki ɗaya da ƙungiyoyin Musulmi da manyan malamai da masana da alƙalai da lauyoyi su kawo mana ɗauki wajen sadaukar da dukiyarsu da don ɗaukaka kalmar Allah wajen ganin Musulmi sun mallaki filin don gina masallaci na zamani a yankin.”
Aminiya ta tuntuɓi Uwargidan marigayin, Madam Nwanne Igwe Orji wacce ta tabbatar da cewa mijinta ya rasu ne a shekarar 2016.
Ta ce “Kafin ya rasu sai da ya miƙa min rubutacciyar wasiyya cewa idan muka tashi sayar da filin mu tabbatar mun sayar ga Hausawan da suke amfani da shi.
“Wannan takarda mai ɗauke da wasiyyar tana tare da ni har yanzu.”
A kan batun cinikin filin ta bayan gida sai ta ce “Wasu mutane ne suka haɗa baki da wasu dangin mijina suka ƙulla cinikin ba tare da sanina ba, kuma suka yi amfani da wasu bara-gurbin jami’an gwamnati suka rusa ginin masallacin da sauran shaguna har da shagona a ciki.
“Amma bayan da muka yi bincike mun gano babu hannun gwamnati a rushe-rushen.
“Hausawan da suke amfani da wannan wuri sun taimaka min ƙwarai wajen fafutikar da muka yi tare zuwa ofishin Kwamandan ’Yan sandan yanki wanda ya tabbatar da gaskiyarmu.
“Saboda haka ina jinjina wa Hausawan kan sadaukar da kansu da ya kai mu ga nasara.”
Madam Nwanne Orji ta tabbatar da cewa sun yi wa filin kuɗi a kan Naira miliyan 200 inda suke fatar Hausawan za su saya don ci gaba da gudanar da ibada a ciki.