Ana neman $396m don yakar yunwa a Arewa Maso Gabashin Najeriya —MDD

Majalisar ta ce yunwar na yin barazana ga rayuwar mutanen yankin.

Ana neman $396m don yakar yunwa a Arewa Maso Gabashin Najeriya —MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana bukatar Dala miliyan 396 cikin gaggawa domin dakile yunwa da rashin abinci mai gina jiki a jihohin Borno da Adamawa da Yobe.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi wannan roko ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis.

A cewar sanarwar, mutane fiye da rabin miliyan na cikin hadarin kamuwa da cutar tamowa, da matsanancin rashin abinci mai gina jiki da kuma mace-mace idan ba a samu karuwar taimakon jin kai ba.

Kimanin yara miliyan biyu ’yan kasa da biyar ne a cikin jihohin uku ke iya fuskantar barazana a bana, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

Ta bayyana hakan a matsayin nau’in rashin abinci mai gina jiki da kuma barazana ga rayuwar mutanen yankin.

Majalisar ta alakanta matsalar karancin abinci da tashe-tashen hankula da rashin tsaro da aka shafe shekaru ana yi a yankin, da kuma hauhawar farashin man fetur da abinci, da karancin Naira a baya-bayan nan da kuma sauyin yanayi.

“Na ga irin bacin ran da iyaye mata ke fama da su na yaki da rayuwar jariransu da ke fama da rashin abinci mai gina jiki a cibiyoyin kwantar da tarzoma da abokan aikinmu ke gudanarwa.

“Wannan al’amari ne da bai kamata kowa ya fuskanta ba,” in ji Matthias Schmale, jami’in kula da ayyukan jinkai na Najeriya.

“Na yi magana da yara wadanda suka bayyana yadda suke tafiya ta kwanaki ba tare da sun ci abinci mai yawa ba.

“Iyaye sun ce ‘ya’yansu sukan kwanta suna kuka saboda yunwa.

“Iyalai na fafutukar ciyar da kansu kamar yadda suka yi watanni ba tare da samun tallafin abinci ba,”in ji shi.

Fred Kafeero, wakilin Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO), ya yi gargadin cewa lokacin rani mai zuwa na iya kara tabarbarewar karancin abinci a tsakanin magidanta masu rauni ba tare da samun hanyoyin rayuwa ta noma ba.

A cewar sanarwar, Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da D lala miliyan 18 domin fara tunkarar matsalar karancin abinci a yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC