‘Ana nuna bambancin addini da siyasa wajen zaben wuraren da ake rushewa a Taraba’
Wasu ’yan kasuwa da Hukumar Raya Birane ta Jihar Taraba ta rusa wa shaguna da wuraren sana’a sun koka cewa ana nuna wariya wajen rushe-rushen da ake yi a garin Jalingo. Alhaji Musa Haruna wanda ya yi magana a madadin wadanda lamarin rushe-rushen ya shafa, ya ce hukumar tana nuna bambancin addini da siyasa wajen […]
Wasu ’yan kasuwa da Hukumar Raya Birane ta Jihar Taraba ta rusa wa shaguna da wuraren sana’a sun koka cewa ana nuna wariya wajen rushe-rushen da ake yi a garin Jalingo.
Alhaji Musa Haruna wanda ya yi magana a madadin wadanda lamarin rushe-rushen ya shafa, ya ce hukumar tana nuna bambancin addini da siyasa wajen zaben wuraren da take rushewa ko wadanda take tayarwa daga wuraren sana’arsu.
Alhaji Musa ya ce shagunan da aka rushe a kusa da masallacin Izala da kuma jama’ar da aka tayar a wuraren sana’arsu a akusa da babban tashar motar Jalingo da wadanda ke kusa da gidan mai na Rano duk an yi ne da nufin musguna wa wani bangare na jama’ar garin.
Ya ce lokacin da ake rushe shagunan kusa da masallacin Izala an turo motoci dauke da ’yan sanda da sojoji rike da manyan bindigogi tamkar za a je yaki. Kuma sun samu labarin an ba jami’an tsaron umarnin wulakata duk wanda ya nemi kawo cikas kan rushe-rushen.
Alhaji Musa ya ce kowa ya san wadanda wuraren kasuwancinsu suka matsi bakin babban titin garin amma saboda su ’yan gatan gwamnati ne an bar su, inda ya kawo misali da wani dan kabilar Ibo da ke baza kayayyakinsa dab da bakin hanya amma saboda yana hulda da manyan jami’an gwamnati an kasa yi masa komai. “Ya kamata gwamnatin jihar ta rika gudanar da harkokinta a kan adalci ba tare da nuna bambancin addini ko kabilanci ba,” inji shi.
A martanin Babban Sakataren Hukumar Raya Birane ta Jihar Mista Major Abba ya musanta zargin, inda ya ce duk shagon da aka rusa ba a gina shi kan ka’ida ba ne. Ya ce gwamnati ce ta bayar da umarnin gudanar da aikin don tsabtace garin Jalingo, inda ya ce ba maganar bambancin addini ko kabilanci a aikin da suke gudanarwa.
Mista Major Abba ya ce yadda ake gina shaguna da wuraren sana’a sun saba wa dokokin raya birane kuma abin da ake yi shi ne a tabbatar cewa duk wani gini ko wurin sana’a an yi shi bisa doka.
Bababn Sakataren ya ce yadda ake gudanar da kasuwanci a babban shataletalen shiga Jalingo yana da hadari ga masu ababen hawa da matafiya da masu gudanar da kasuwancin. Kuma irin wadannan matasaloli suka sa aka tayar da masu kasuwanci a wurin da sauran wurare makamantansu.
A wani labarin, wani dan kasuwa a garin Jalingo fadar Jihar Taraba, mai suna Umaru Garba ya kai gwamnatin jihar gaban Hukumar Hukumar Sauraron Koke-koken Jama’a, don a bi masa hakki kan rushe shugunansa 24 da aka yi
Malam Umaru Garba ya shaida wa wakilinmu cewa, kafin ya soma ginin shagunan sai da ya samu izini daga Hukumar Kula da Gine-Gine ta jihar, bayan ya sayi filin daga hannun Mista Simon Bodi Jen a kan Naira miliyan biyu da rabi. Ya ce wanda ya sayar masa da filin ma’aikaci ne a Ma’aikatar kasa da Safiyo kuma filin yana da duk takardun da suka kamata.
“Ganin filin na da takardu ya sa na soma ginin, amma sai kawai aka wayi gari an turo motocin rushe gine-gine tare da jami’an tsaro aka rushe min ginin” inji shi.
Ya ce ya je ofishin ’yan sanda na GRA a Jalingo ya bayar da rahoton barnar da ake yi masa, amma babu matakin da suka dauka a kai, kuma a lokacin kotuna suna yajin aiki wannan ya sa ya kai kara ga hukumar.
Ya ce fin karfi kawai aka nuna masa aka rusa ginin saboda ba a ba shi wani umarni na baki ko a rubuce cewa ya dakatar da ginin ba.