Ana rushe-rushe ne don yin gyara – Kwamishina
Gwamnatin Jihar Kano ta mayar da martani ga korafin da jama’ar jihar ke yi kan rushe-rushe da take shirin yi inda aka fara shafa jan fenti a gidajensu.Kwamishinan kasa da Safiyo na Jihar Alhaji Muhammad Nadu Yahaya ya ce gwamnatin ta yi haka ne da nufin gudanar da gyare-gyare a wasu unguwanni da ke birnin […]
Gwamnatin Jihar Kano ta mayar da martani ga korafin da jama’ar jihar ke yi kan rushe-rushe da take shirin yi inda aka fara shafa jan fenti a gidajensu.
Kwamishinan kasa da Safiyo na Jihar Alhaji Muhammad Nadu Yahaya ya ce gwamnatin ta yi haka ne da nufin gudanar da gyare-gyare a wasu unguwanni da ke birnin Kano da dorayi da Ja’en da Gaida saboda yadda unguwannin suke a cunkushe. “Duk wanda zaune a unguwannin Gaida da dorayi ya san tun farko yanka filayen awon igiya ne, babu hannun gwamnati a ciki. Mutane suna zaune a cikin kunci da rashin walwala hakan ya sa gwamnati ta waiwaye su don gudanar da wasu gyare-gyare a unguwannin,” inji shi.
Kwamishinan ya ce gwamnati tana shan wahala wajen samar wa mutanen wadannan yankuna ababen more rayuwa.
Ya roki jama’ar unguwannin da gyare-gyaren zai shafa su yi hakuri saboda a duk lokacin da aka tashi gyara sai an bata wa wani rai.
Game da batun raba filaye a jihar, Kwamishinan ya ce daga yanzu babu sauran filayen awon igiya da za a rika bayarwa a jihar. “A yanzu kokarin da muke shi ne na hana yanka filayen awon igiya a fadin Kano shi ya sa tun zuwan wannan gwamnati muka yanke cewa za mu yi kokarin samar da filaye dubu 100 a cikin shekara hudun da za mu yi a kan mulki. Kuma filayen da gwamnatin ke rabawa, karami girmansa shi ne ya kasance mai murabba’in kafa 30 zuwa 40,” inji shi.