Ana sace kusan Naira tiriliyan bakwai duk shekara daga Najeriya – Rahoton EU

Shugabannin kungiyar Tarayyar Afirka (AU) sun amince da rahoton Kwamitin Thabo Mbeki kan Muguwar Ta’asar Satar Dukiyar Jama’a da ake yi a Afirka, inda aka gano ana sace kimanin Dala biliyan 40 da miliyan 900 (kimanin Naira tirilyan shida da biliyan 870) daga Najeriya duk shekara. A ranar Lahadin da ta gabata ne shugabannin kasashen […]

Ana sace kusan Naira tiriliyan bakwai duk shekara daga Najeriya – Rahoton EU
Ana sace kusan Naira tiriliyan bakwai duk shekara daga Najeriya – Rahoton EU

Shugabannin kungiyar Tarayyar Afirka (AU) sun amince da rahoton Kwamitin Thabo Mbeki kan Muguwar Ta’asar Satar Dukiyar Jama’a da ake yi a Afirka, inda aka gano ana sace kimanin Dala biliyan 40 da miliyan 900 (kimanin Naira tirilyan shida da biliyan 870) daga Najeriya duk shekara.

A ranar Lahadin da ta gabata ne shugabannin kasashen suka amince da rahoton kwamitin a taron da suka gudanar a Addis Ababa fadar kasar Habasha, inda kwamitin ya gano daga cikin kimanin Dala biliyan 60 (kimanin Naira tiriliyan 10 da miliyan 80) da ake sacewa daga Afirka fiye da biyu uku na kudin daga Najeriya ake sace su.
Rahoton ya ce ana sace kudin ne ta hanyar cin hanci da almundahana da kauce wa biyan haraji da fitar da kudi da riba ta haramtacciyar hanya da manyan kamfanonin kasashen duniya suke yi.
Najeriya ce kasa ta bakwai a arzikin man fetur a duniya, kuma tana asarar kimanin kashi 68 da digo daya na daukacin kudin shigar da Afirka take asara a kowace shekara sakamakon fitar da kudaden shiga ta haramtacciyar hanya zuwa kasashen waje.
Najeriya dai tana hako ganga miliyan biyu da dubu 300 na danyen mai a kullum, inda ta zamo kasa mafi hakar mai a Nahiyar Afirka, sai dai duk da haka tana fama da matsanancin talauci da rashin ci gaba.
Sauran kasashen da ake tafka satar dukiyar jama’a sun hada da Masar inda aka yi kiyasin ans sace Dala biliyan 28 da digo biyu da Moroko inda ake sace Dala biliyan 20 da digo uku.
Jimillar kudin da aka sace daga Najeriya daga 1970 zuwa shekarar 2008 ya kai Dala biliyan 217 da digo bakwai, (kimanin Naira tiriliyan 36 da biliyan 570) wato kimanin kashi 30 da rabi na kudin da aka sace daga Nahiyar Afirka, sai Masar an sace Dala biliyan 105 da digo biyu, (kimanin Naira tiriliyan 17 da biliyan 670) wato kashi 14 da digo bakwai na daukacin kudin da aka sace daga Afirka. Afirka ta Kudu kuma an sace Dala biliyan 81 da digo takwas (kimanin Naira tirilyan 13 da biliyan 740) wato kashi 11 da digo 4.
Damuwa da muguwar satar da ake tafkawa da aka gano a shekarar 2011 wadda kuma take barazana ga cimma nasarar bunkasa kasashe na shirin muradun karni, ya sa a taron hadinn gwiwa na 4 na ministocin tattalin arziki da tsare-tsare tsakanin Tarayya Afirka da Hukumar Tattalin Arziki ta Majalisar dinkin Duniya mai kula da Nahiyar Afirka (AUC/ECA) suka kafa kwamitin Mbeki domin nazarin abubuwan da suke kawo cikas ga ci gaban Afirka.
Kwamitin ya kuma bukaci Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya da sauran shugabannin kasashen Afirka su fito fili su bayyana wa duniya dukiyar da suka mallaka kuma su ba jama’a damar tantance dukiyar domin a dakile almundahana da satar dukiyar jama’a da shugabannin suke yi.