Ana samun nasarar yaki da cin hanci da rashawa a Saudiya – Atoni Janar
Atoni janar na kasar Saudiyya ya ce gwamnati ta kwato kudi fiye da dala biliyan 106 a karkashin shirinta na yaki da cin hanci da rashawa karkashin Yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman. Sheik Saud al Mojeb ya ce daga cikin mutum 381 da aka kira a watan Nuwamban da ya gabata domin amsa […]

Atoni janar na kasar Saudiyya ya ce gwamnati ta kwato kudi fiye da dala biliyan 106 a karkashin shirinta na yaki da cin hanci da rashawa karkashin Yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman.
Sheik Saud al Mojeb ya ce daga cikin mutum 381 da aka kira a watan Nuwamban da ya gabata domin amsa wasu tambayoyi, har yanzu ana tsare da 56 daga cikinsu kamar yadda BBC ta ruwaito.
Ya ce an wanke sauran daga aikata laifi yayinda aka saki wasu bayan da suka amsa aikata laifi tare da mika kadarorinsu da kudi ga gwamnati.
Sai dai Sheik Mojeb bai bayanna sunnayen wadanda ake zargi ba, sai dai rahotanni sun ce a cikinsu akwai yarimomi da ministoci da kuma ‘yan kasuwa.
A kwanakin baya ne aka sako hamshakin dan kasuwanan nan Yarima Alwaleed bin Talal da kuma Alwalid al Ibrahim, wanda ya mallaki kafar watsa shirye shirye ta MBC daga otel din Ritz-Carlton da ke garin Riyadh inda ake tsare da su.
Sai dai mutanen biyu sun musanta zargin da ake yi mu su amma kuma wasu majiyoyi na gwamnatin Saudiyyar sun ce mutunen sun amince su bada wasu kudade bayan da suka amince da aikata laifin da ake zarginsu da shi.
Sauran da ake tsamanin cewa an sako su sun hada da Yarima Mitleb bin Abdullah wanda da ne ga mariyagi sarki Abdullah wanda majiyoyin suka ce ya mika kadarori da aka yi kiyasin cewa adadinsu ya wuce dala biliyan daya da kuma Ibrahim al Assaf wanda minitsa ne wanda kuma rahotani suka ce ba a same shi da laifi ba.
Sai dai Sheik Mojen ya ce ya ki cimma masalaha da sauran mutane 56 da ake tsare da su saboda binciken da ake cigaba da yi akansu game da zargin cin haci da rashawa.
Ana dai tsamammin cewa an wuce da su zuwa wani gidan yari daga otel din Ritz Carlton da ake tsare da su wanda za a sake bude wa a watan gobe. A makon da ya gabata ne dai ministan kudi na kasar Mohammed al Jadaan ya ce za a yi amfani da kudaden da aka kwato a wani shiri da aka ware ma kudi dala biliyan 13 domin tallafawa ‘yan Saudiyya samun saukin tsadar rayuwa.
Sai dai wasu masana sun soki shirin yaki da cin hanci da rashawa na Yarima mai jiran gado Mohammen bil Salman mai shekara 32 wanda da ne ga sarki Salman, inda suka bayyana shi a matsayin wani shiri na neman iko.