Ana samun raguwar masu kamuwa da Coronavirus a Najeriya
Kar a manta masu dauke da kwayoyin cutar Coronavirus ba sa nuna wasu alamu da za a gane.
Karfin cutar Coronavirus na ci gaba da raguwa a Najeriya kamar yadda alkaluman Hukumar Dakile Cututtuka masu yaduwa a kasa (NCDC) suka nuna.
A yanzu an shafe fiye da mako daya kenan ba tare da cutar Coronavirus ta yi kisa ba a kasar. Haka kuma jimillar masu kamuwa duk rana na ci gaba da raguwa sabanin yadda ake samun dubbai ko daruruwa a baya.
- Matar da ta fi kowa tsufa a Amurka ta mutu bayan shafe shekara 116 a duniya
- Getafe ta rike wuyan Real Madrid a La Liga
Jimillar mutum 2,061 cutar ta kashe tun bayan bullarta a Najeriya kuma tun Lahadin makon da ya gabata zuwa Lahadin jiya ba a samu wanda yam utu sakamakon cutar ba.
Alkaluman da NCDC ta fitar a jiya Lahadi sun nuna cewa an samu karin mutum 26 sabbin kamuwa da cutar, inda a yanzu adadin wadanda suka harbu a kasar ya kai 164,233.
Jihar Ebonyi ce a kan gaba da mutum 10, sai Legas inda cutar ta fi kamari a duk fadin kasar da mutum 9.
Haka kuma an samu mutum biyu sabbin kamuwa da cutar a Abuja, babban birnin kasar, sai Jihar Kano da Osuna inda nan ma aka samu mutum biyu-biyu da kuma Oyo mai mutum daya.
Sai dai duk da haka, NCDC na ci gaba da gargadin al’ummar Najeriya a kan tsaftace muhalli da sauran wuraren zamansu domin dakile yaduwar a zamantakewarsu.
NCDC tana mai cewa a ci gaba da kiyaye matakan kariya da mahukuntan lafiya suka shar’anta na bayar da tazara da kauracewa shiga taron jama’a, wanke hannu da sabulu a kai a kai karkashin ruwa mai gudana ko kuma a yi amfani da sunadarin tsaftace hannu.
Ta kuma tunatar da muhimmancin sanya takunkumin rufe fuska, inda take ankarar da al’umma a kan cewa mafi akasari masu dauke da kwayoyin cutar ba sa nuna wasu alamu da za a iya gane su cikin jama’a.