Ana sayar da buraguzan ginin Kaaba kan (Riyal Dubu 150) Naira miliya 9

Ana yin fasakwaurin buraguzan tubulan masallatai masu alfarma, a lokacin da ake aikin fadada su, inda aka kasuwar bayan fage ake sayar da su kan Riyal dubu 150. Kuma wadanda suka fi sayen bagalcen ginin sun hada da masanan tarihi da masu tara kayan tarihi da masu sha’awa, kamar yadda jaridar nazarin tattalin arziki ta […]

Ana sayar da buraguzan ginin Kaaba kan (Riyal Dubu 150) Naira miliya 9
Ana sayar da buraguzan ginin Kaaba kan (Riyal Dubu 150) Naira miliya 9

Ana yin fasakwaurin buraguzan tubulan masallatai masu alfarma, a lokacin da ake aikin fadada su, inda aka kasuwar bayan fage ake sayar da su kan Riyal dubu 150. Kuma wadanda suka fi sayen bagalcen ginin sun hada da masanan tarihi da masu tara kayan tarihi da masu sha’awa, kamar yadda jaridar nazarin tattalin arziki ta Al-Ektisadiyah ta ruwaito.

Hukumar kula da manyana masallatai masu alfarma, ta bayyana cewa, ta ttara dukkan bayanai da hotunan masallatan a rumbun adana bayanan sadarwa, don alkinta tariohi a daidai lokacin da ake aikin fadada masallatan.
Mai magana da yawun hukumar, Ahmad Al-Mansouri ya ce daukacin bayanan masallatan har ma da turakun hasumiya an riga an tattara bayanansu, an alkinta su.
“Mun fara tattara bayanai tun a shekarar 2006. Kuma wannan hukuma ta taba gudanar da baje kolin zayyanar masallatai masu alfar tun a shekarar 1999. An kuma gudanar da baje kolin ne a kusa da masakar rigar Kaaba, wato Kiswa. A halin yanzu mun kammala aikin fadada wurin don haka za a hada da sababbin kayan tarihi,” a cewarsa.
Wata majiya ta bayyana cewa, bakin da ke aikin fadada masallatan su ne ke kai buraguzan ginin kasuwar bayan fage. daya daga cikin majiyar ta ce
“Kowane balgacen gini yana da kimar darajarsa a kasuwa. Alal misali balgacen da aka samo daga rijiyar zamzam, wadda aka gine a shekarar 1954, zamanin mulkin sarki Saud Bin Abdulaziz kimar kudinsa ya kai Riyal dubu shida.
“Shi kuwa farin karfen da ake kyautata zaton da shi aka rufe sawun Annabi Ibrahim, kimar kudins at akai Riyal Dubu 150,” inji shi.
Ya ce masu sayen wadannan kayayyakin balgattun gini, sun hada da masanan tarihi da masu tattara kayan tarihin da suka shafi al’adun Musulunci da kuma masu sha’awa. “Wannan al’ada ta samo asali ne tun a daular Usmaniyya ta Turkawa, wadanda ke da tushe a kasar Saudiyya. Wadannan balgace gine-gine na nuni da irin halin da masallatan suka shiga tsawon tarihin su.
“Suna sayar da bagalcen gini ga abokan huldarsu a farashi mai rahusa, su kuma su sayar da su ga masu tattara kayan tarihi da masu nazarin tarihin Musulunci da kuma amsu sha’awa. Sukan yi wannan shirin ne ta yadda ba za a gane cewa buraguzan ginin sun bace ba.