Ana share tan 143 na shara a Masallacin Harami a kullum
A kullum ana share sharar da ta kai nauyi tan 143 (kimanin Kilogram dubu dari da 30) daga Masallacin Harami da ke kasar Saudiyya, kamar yadda kafar yada labarai ta Arab News ta bayyana ranar Talata. Wannan yana nufin nauyin sharar da ya kai tan 143, akalla zai cika tirela hudu zuwa biyar.Rahoton ya kuma […]
A kullum ana share sharar da ta kai nauyi tan 143 (kimanin Kilogram dubu dari da 30) daga Masallacin Harami da ke kasar Saudiyya, kamar yadda kafar yada labarai ta Arab News ta bayyana ranar Talata.
Wannan yana nufin nauyin sharar da ya kai tan 143, akalla zai cika tirela hudu zuwa biyar.
Rahoton ya kuma ce akalla mutum 2,500 ne suke gudanar da aikin tsaftace masallacin a kullum.
Darakta da ke kula da tsaftar masallacin Maher al-Zahrani ya ce a kullum ma’aikatan na gudanar da aikinsu a daidai lokacin da masu ibada suke ci gaba da ibadunsu. Ya ce: “Muna da shinfidu da suka kai guda dubu 17. Zan yi amfani da wannan damar wajen jan hankalin masu ibada da cewa idan za su ci abinci a cikin masallacin, ba a hana su ba, amma kada su bata shi da shara.” Daga karshe ya ce za a ci gaba da raba wa masu ibada ruwan zam-zam da dabino da kuma ruwan shayi a lokacin buda baki.