Ana sheka ruwa kasaa na shanyewa
Edita Aminiya mai farin jini a yau ina tsokaci ne a kan taron wuni biyu da masu ruwa da tsaki suka yi a birnin Maiduguri fadar GwamnatinJihar Borno, domin tallafawa, da kuma sake gina matsugunnin wadanda rikicin masu tada kayar baya ya daidaita a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya. Hakika an dade ana sheka ruwa, […]
Edita Aminiya mai farin jini a yau ina tsokaci ne a kan taron wuni biyu da masu ruwa da tsaki suka yi a birnin Maiduguri fadar GwamnatinJihar Borno, domin tallafawa, da kuma sake gina matsugunnin wadanda rikicin masu tada kayar baya ya daidaita a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya. Hakika an dade ana sheka ruwa, amma kasa tana shan shanyyewa, ma’ana an dade ana ware makudan kudi da sunan za a tallafa mana, amma sai dai mu ji ana yayatawa a gidan rediyo. Sabili da wadanda ake danka wa kudin galibinsu azzalumai ne. Kuma kashin dankali suke yi da kudin tallfin. Amma muna kyautata zaton cewa, wannan karon rabon tallafin zai bambanta da sauran lokutan da ya gabata. Domin kuwa duniya ta sanya ido don ganin kowane dan gudun hijira ya amfana da kudin agajin. Har ila yau, muna addu’ar Allah ya sa tallafin ya shiga hannun wadanda aka yi domin su, ba hannun azzalumai ba amin. Kana daga karshe muna rokon Allah ya kawo mana karshen matsalar rashin tsaron da ta addabi kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran sassan kasashen yankin Sahel baki daya amin. Daga Adamu Aliyu Ngulde, Daga Jihar Borno 07083336622 08032135939. [email protected]