Yadda ake shigo wa ’yan bindiga da makamai Najeriya

Gwamna Jihar Zamfara Bello Matawalle ya bayyana yadda ’yan bindiga ke safarar makamai zuwa cikin Najeriya duk da cewa an rufe iyakokin kasar. A ganawarsa da Firaministan Jamhuriyar Nijar Brigi Refini domin haka kai wajen yakar ayyukan ’yan bindiga da sauran miyguan laifuka a yankin, Matawalle ya ce ’yan bindigar sun sauya salonnsu na fasakwaurin […]

Yadda ake shigo wa ’yan bindiga da makamai Najeriya

Gwamna Jihar Zamfara Bello Matawalle ya bayyana yadda ’yan bindiga ke safarar makamai zuwa cikin Najeriya duk da cewa an rufe iyakokin kasar.

A ganawarsa da Firaministan Jamhuriyar Nijar Brigi Refini domin haka kai wajen yakar ayyukan ’yan bindiga da sauran miyguan laifuka a yankin, Matawalle ya ce ’yan bindigar sun sauya salonnsu na fasakwaurin makamai zuwa Neriya.

“Muna sane da cewa matsin da masu fasakwaurin makamai a kan ababen haka kwa fuskanta ya sa yanzu sun koma amfani da rakuma.

“Na yanke hukuncin taimakawa da motocin sintiri guda biyar baya ga kananan jirage marasa matuka da aka ba wa masu tsaron iyakar Nijar”, inji gwamnan.

Ya nuna jin dadi da amsa kiran da Firaminista Refini ya yi, sannan ya ce Shugaban Buhari “Ya yi farin ciki da zuwanka yana kuma fatan alheri.

“Ya kuma sa in gayyace ka domin a ci gaba da taimaka wa kawo karshen fashin daji a kasashen biyu”.

Gwamnan ya kuma mika masa kokon baran Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, na cewa Jamhuriyar Nijar ta taimaka ta toshe hanyoyin safarar makamai zuwa Najeriya.

A nasa bangaren Firaministan ya nuna jin dadi kan yunkurin hada kai tsakanin Najeriya da kasarsa wajen yakar manyan laifuka a tsakanin iyakokin kasashen biyu.

Ya kara da cewa abun da Najeriya ke fama da shi na matsalar ’yan fashin daji da ta’addanci ba bako ba ne ga kasarsa.

Jamhuriyar Nijar ma na fama da matsalolin ta fuskoki daban-daban daga ‘Boko Haram da ’yan tayar da kayar Baya da ga Mali da Burkina Faso.

Bakon ya yaba kokarin gwamanman wurin kawo kawancen da zai lalubo hanyoyin da ma dabarun magance matsalar.