Ana shirin korar ma’aikatana kananan hukumomi kan kin zaben PDP a Taraba
Ma’aikatan kananan hukumomin Jihar Taraba sun yi zargin cewa gwamnatin jihar ta dauko hanyar korar wasu daga cikinsu bisa zargin cewa ba su zabi Jam’iyyar PDP a lokutan zaben Shugaban kasa da na Gwamna ba. Wasu daga cikin ma’aikatan da suka zanta da wakilinmu da suka nemi kada a fadi sunansu sun ce tuni har […]
Ma’aikatan kananan hukumomin Jihar Taraba sun yi zargin cewa gwamnatin jihar ta dauko hanyar korar wasu daga cikinsu bisa zargin cewa ba su zabi Jam’iyyar PDP a lokutan zaben Shugaban kasa da na Gwamna ba.
Wasu daga cikin ma’aikatan da suka zanta da wakilinmu da suka nemi kada a fadi sunansu sun ce tuni har an bayar da sunayen wadanda za su maye gurabensu a wadanda za a kore su daga aiki.
Ma’aikatan sun yi zargin cewa yunkurin korarsu daga aiki wata hanya ce ta nuna wa mabiya wani addini bambanci tare da nuna bambancin kabila amma aka fake da siyasa.
Ma’aikatan sun yi zargin cewa kananan hukumomin da suke arewa da tsakiyar jihar ne korar za ta fi shafa, duk da dai akwai kananan hukumomi biyu da abin zai shafa a kudancin jihar.
“An fada mana a fili cewa za a kore mu daga aiki bisa zargin da ake yi mana cewa ba mu zabi Jam’iyyar PDP ba,” inji daya daga cikin wadanda ake yi wa barazanar kora daga aikin.
Bincikin wakilinmu ya gano cewa barazanar ba ta tsaya kan ma’aikatan kananan hukumomin kawai ba, har ma da ma’aikatan gwamnatin jihar.
Majiyarmu ta ce kafin zaben Mukaddashin Gwamnan Jihar Alhaji Sani Abubakar danladi ya ba manyan ma’aikatan kananan hukumomi da na gwamnatin jihar umarnin cewa dole su tabbatar an zabi PDP a garuruwansu.
Da wakilinmu ya tuntubi kakakin Ma’aikatar kananan Hukumomi da Masarautu ta Jihar, Mista Emmanuel Ukwen kan wannan zargi, ya ce bai da labarin za a kori wani ma’aikaci daga wata karamar hukumar jihar.
A wata sabuwa, Jami’yyar APC ta yi barazanar kai gwamnatn Jihar Taraba kotu kan nada shugabannin riko a kananan hukumomi 16 na jihar.
Shugaban Jam’iyyar Alhaji Hassan Ardo ya ce nadin ya saba wa tsarin mulkin kasar nan saboda haka ba za su bari a yiw a tsarin mulkin kasa zagon kasa ba.
Alhaji Hassan Ardo ya ce tsarin mulkin kasa ya nuna karara cewa kafin wa’adin mulkin shugabannin kananan hukumomi ya kare dole ne a gudanar da zaben wadanda za su maye gurbinsu.
Ya zargi gwamnatin Jihar Taraba da kin bin dokar kasa a mafi yawan harkokinta, inda ya ce dole ne a tilasta wa gwamnatin ta bi doka a harkokin gudanar da mulkin jihar.
A ranar 17 ga watan ne wa’adin mulkin shugabannin kananan hukumomin jihar ya kare kuma Mukaddashin Gwamnan ya zabi sunayen wadanda za su shugabancin kananan hukumomin a matsayin riko ya tura wa majalisar jihar don amincewa a ranar Litinin da ta gabata, inda majalisar ta amince kuma aka rantsar da su da misalin karfe 3:00 na wannan rana.