Ana shirin kwaso ’yan Najeriya daga Afirka ta Kudu

Bianca ta tunatar da irin rawar da Najeriya ta taka wajen taimaka wa gwagwarmayar neman ‘yancin Afirka ta Kudu.

Ana shirin kwaso ’yan Najeriya daga Afirka ta Kudu

Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin dawo da ’yan ƙasar da ke zaune a Afirka ta Kudu zuwa gida, biyo bayan hare-haren ƙiyayya kan baƙi da aka riƙa kai musu a makonnin da suka gabata.

Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu ta sanar da shirin duba yiwuwar dawo da ’yan ƙasar da ke da ra’ayin koma wa gida daga Afirka ta Kudu sakamakon ƙaruwar hare-hare da ake kai wa baƙi.

Jami’ar diflomasiyyar ta ce tuni aka samu ’yan Najeriya kusan 130 da suka bayyana aniyar komawa gida, kuma ana sa ran adadin zai iya ƙaruwa nan gaba.

Madam Odumegwu-Ojukwu ta kuma jaddada cewa ba za a taɓa lamunta ba rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya da ke zaune a Afirka ta Kudu su ci gaba da kasancewa cikin haɗari.

Ministar ta ce rashin tabbas ya ƙaru cikin ‘yan makonnin nan sakamakon zanga-zangar ƙin jinin baƙi, inda wasu ɓata-gari a Afirka ta Kudu suke far wa ‘yan Najeriya a wasu birane.

Bugu da ƙari ministar ta bayyana cewa aƙalla ’yan Najeriya biyu ne suka mutu sakamakon lamarin na baya-bayan nan, inda ta yi zargin cewa wadannan halaye na nuna ƙiyayya ga baƙi sun sake tasowa ne gabanin zaben Afirka ta Kudu, inda jam’iyyun adawa masu ƙyamar baƙi ke amfani da yanayin domin samun ƙuru’in jama’a musamman matasa marasa aikin yi.

Ta ce Amamiro Emmanuel ya mutu ranar 25 ga watan Afrilu sakamakon raunin da aka ce ya ji bayan dakarun tsaron Afirka ta Kudu sun lakaɗa masa duka a birnin Port Elizabeth.

An ba da rahotonm cewa Nnaemeka Andrew, a cewarta, ya mutu bayan ya haɗu da ‘yan sandan cikin gari na Tshwane, inda aka samu gawarsa a babban wurin ajiye gawarwaki na Pretoria ranar 20 ga watan Afrilu.

“Wannan wani abin Allah wadai ne kuma abin da ba za a lamunta ba ne. Ofishin jakadancin Najeriya na bibiyar bincike kan waɗannan abubuwan baƙin cikin sahu da ƙafa, kuma Najeriya na neman a tabbatar da adalci a kan waɗannan lamurran,” in ji ta.

Ministar ta kuma bayyana cewa ana tsammanin wata zanga-zanga tsakanin ranar 4 zuwa 8 ga watan Mayu, lamarin da ya sa Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin sa ido kan lamarin.

Ta ƙara da cewa ofisoshin jakadancin Najeriya a Afirka ta Kudu suna ci gaba da tuntuɓar juna da hukumomi na cikin ƙasar domin rage barazana ga ‘yan ƙasar.

Odumegwu-Ojukwu ta tunatar da irin rawar da Najeriya ta taka wajen taimaka wa gwagwarmayar neman ‘yancin Afirka ta Kudu, tana mai gargaɗin cewa ya zama wajibi a daina barazana ga rayuka da hajojin ‘yan Nijeriya.

“Muna jajircewa wajen aiki da Afirka ta Kudu domin neman hanyoyin kawo ƙarshen wannan yanayi na ƙin jinin baƙin,” in ji ta, tana mai cewa kwanan baya ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya kan kare ‘yan ƙasashen biyu.