Ana shirin mayar da Suntai asibitin waje
Ana shirin sake komawa da Gwamnan Jihar Taraba Mista danbaba Suntai wani asibiti da ke kasar waje don ci gaba da jinyarsa.Gwamna danbaba Suntai wanda wata majiya a fadar gwamnatin jihar da ke Jalingo ta bayyana wa wakilinmu cewa na cikin mummunan halin rashin lafiya, ta ce yanayin jikin Suntai ne ya sa ’yan uwansa […]
Ana shirin sake komawa da Gwamnan Jihar Taraba Mista danbaba Suntai wani asibiti da ke kasar waje don ci gaba da jinyarsa.
Gwamna danbaba Suntai wanda wata majiya a fadar gwamnatin jihar da ke Jalingo ta bayyana wa wakilinmu cewa na cikin mummunan halin rashin lafiya, ta ce yanayin jikin Suntai ne ya sa ’yan uwansa suka nemi Mukaddashin Gwamnan Jihar Alhaji Sani Abubakar danladi ya bayar da kudi don a koma da Gwamnan asibiti don ci gaba da yi masa jinya.
Majiyar ta kara da cewa Mukaddashin Gwamnan Jihar ya ba Ma’aikatar Kudi ta Jihar umarni ta bayar da kudi don kai danbaba Suntai asibiti a kasar waje.
Wannan na zuwa ne duk da ikirarin da wasu na kusa da Suntai su ka yi tayi a baya cewa yana da isasshiyar lafiyar da zai iya komawa bakin aiki.
Haka din a cewar majiyar ya tona asirin irin wadannan mutane da suka yi ta yada bayanai na karya kan lafiyar danbaba Suntai.
Mista Bulus James wani mazaunin Jalingo ya ce ashe dama karya a ka yi ta fada musu cewa tsohon Mukaddashin Gwamnan Jihar Alhaji Garba Umar ya ki bai wa danbaba Suntai ragamar mulki.
Ya ce ga shi kusan wata uku ke nan da aka cire Alhaji Garba Umar har yanzu ba a mika wa Suntai ragamar mulki ba.
Mista Bulus James ya ce an yaudari jama’ar jihar ta hanyar amfani da addini da kabilanci kan maganar rashin lafiyar danbaba Suntai, to, amma yanzu gaskiya ta yi halinta kowa ya san gaskiya.
Ya ce wadanda suka tsaya kai da fata cewa Suntai na da cikakkiyar lafiya yanzu sun manta da maganar danbaba Suntai sun karbi mukamai suna shan lagwadar mulki.
kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin likitan danbaba Suntai, Dokta Ahmed Kara ya ci tura domin ya ki amsa kira da kuma sakon tes da wakilinmu ya aika masa.