Ana Son A Naɗa Betta Edu Sabon Muƙami A Gwamnatin Tinubu

Hakan dai na zuwa watanni biyu bayan dakatar da Betta Edu daga muƙaminta.

Ana Son A Naɗa Betta Edu Sabon Muƙami A Gwamnatin Tinubu

Betta Edu, Ministar Jinkai da Yaki da Fatara

Rahotanni sun bayyana cewa wasu masu faɗa a ji a ƙasar na neman dawo da dakatacciyyar Ministar Harkokin Jin-ƙai da Yaƙi da Fatara, Betta Edu kan madafan iko.

Hakan dai na zuwa watanni biyu bayan dakatar da Betta Edu daga muƙaminta.

Kawo yanzu dai Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziki Zagon Kasa EFCC da kuma Fadar Shugaban Kasa sun bar ‘yan Najeriya cikin duhu kan mataki na gaba.

Binciken da wakilinmu ya yi a ƙarshen mako ya nuna cewa, bayan dakatar da Edu da binciken da hukumar ta EFCC ta yi a ranar 8 ga watan Janairu, mun gano cewa hukumar ta gudanar da cikakken bincike, kuma tuni ta miƙa rahoton wucin gadi ga fadar shugaban kasa.

An samu labarin cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta miƙa rahoton wucin gadi na binciken da ta yi kan zargin da ake yi wa ministar da aka dakatar, inda ta ba da shawarar a gurfanar da Edu a gaban kuliya.

Sai dai kuma idan aka yi la’akari da irin rawar Betta Edu ta taka wajen samun nasarar jam’iyyar APC mai mulki, akwai zargin cewa wasu masu faɗa a ji ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, na matsin lamba ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ya yi duk mai yiwuwa wurin ganin ba a hukunta ta ba.

Binciken da muka yi ya bankaɗo cewa akwai masu roƙon cewa Tinubu ya sake bai wa Edu wani muƙami, ba sai lallai muƙamin minista ba.

Abin da hakan ke nufin dai shi ne a binne wannan batu da ya yi sanadiyar dakatar da ita, a kwarari gaba.

‘EFCC ta wanke Halima Shehu’

Mun kuma gano cewa, Hukumar EFCC ta wanke Shugabar Hukumar Kula da Zuba Jari ta Kasa (NSIPA) da aka dakatar, Halima Shehu.

Wannan tsarki da EFCC ta yi wa Halima na ƙunshe a wani rahotonta na wucin gadi, kamar yadda majiyarmu ta tabbatar mana.

“Takardun da aka bankaɗo game da ayyukan da Halima ta yi a NSIPA, EFCC ta binciki bayanan da aka bankaɗo.

“An gano cewa haƙiƙa ta bi ƙa’idojin da suka kamata wurin rarraba kuɗaɗen da aka zarge ta dangane da su saboda duk bangarorin da abin ya shafa sun amince da sa hannunsu.”

“An gano cewa an fitar da kuɗaɗen ne saboda dalilan da aka ware su. Ban da haka, Halima ta ci gaba da biyan kuɗin ne a daidai inda waɗanda suka riƙe ofishin suka tsaya.”

Rahoton ya bayyana cewa Halima ta biya waɗannan kuɗaɗen ne domin gujewa yi wa doka karan-tsaye

“Kuma an yi hakan ne don gujewa keta doka, domin ‘yan kwangilar sun gabatar da duk takardun da suka dace.”

Dangane da buƙatar EFCC na nema a gurfanar da Betta Edu, majiyarmu ta ce “Wani mutum mai karfin fadi a ji a Villa bai ji daɗin rahoton na EFCC ba, don haka ya ce waɗanda suka kawo shi su mayar da shi su sake nazari a kai.”

Amma da aka muka nemi jin sahihancin ikirarin na cewa an miƙa rahoton wucin gadi ga shugaba Tinubu, Dele Oyewale, mai magana da yawun hukumar ta EFCC, ya shaida wa Aminiya cewa har yanzu ana ci gaba da bincike kan lamarin.

Da aka tambaye shi lokacin da za a kammala binciken, la’akari da cewa majiya mai tushe ta tabbatar da gabatar da rahoton wucin gadi, Oyewale ya ki yin ƙarin bayani.

A nasa bangaren, lokacin da aka tuntuba kan zargin cewa Akpabio yana aiki tuƙuru don ganin an wanke waɗanda ake zargin, Eseme Eyiboh mai magana da yawun Shugaban Majalisar Dattawan, ya ce, Betta Edu ba ta taba zama a majalisa ba, ita ba ministar da shugaban Majalisar Dattawa ya naɗa ba ce don haka ba ruwan mai gidansa da wannan batu.

Binciken da wakilinmu ya gudanar a hukumar ta EFCC ya nuna cewa, ba a sanya sunayen jami’an da aka dakatar da su domin gurfanar da su gaban kuliya ba, wanda hakan na daga cikin hurumin da ya rataya a wuyan hukumar, kamar yadda dokar da ta kafa ta ta tanada.

Betta Edu ta faɗa cikin matsala ne bayan da wata takarda ta bayyana a intanet, inda ta buƙaci Akanta-Janar ta Najeriya, Oluwatoyin Madein da ta tura kuɗi har Naira miliyan 585 zuwa wani asusu mai zaman kansa.

Bayan haka kuma, wasu takardun da ta amince da su, ciki har da amincewa da kuɗin jirgin zuwa Kogi, duk da cewa babu filin sauka da tashin jiragen sama ko ɗaya a jihar da ba ta da filin jirgin sama

Idan ba a manta ba, waɗannan takardu sun ta da yamutsi, lamarin da ya sa Shugaban Kasa ya dakatar da ita.