Ana ta tafka shari’ar wata ’yar Sudan kan rashin lullube kanta

Wata ’yar Sudan za ta fuskanci hukuncin bulala a kotu, bayan da ake ta tafka shari’a kan keta dokar sutura ta kamala da Gwamnatin Sudan ta kafa tun a shekarar 1989, bayan da aka sameta da laifin rashin lullube kanta. Tun a cikin watan Satumbar bana aka fara shari’ar Amira Osman Hamid, inda lauyyanta ya […]

Ana ta tafka shari’ar wata ’yar Sudan kan rashin lullube kanta

TO GO WITH AFP STORY BY IAN TIMBERLAKE Sudanese Amira Osman Hamed speaks with an AFP journalist during an interview in Khartoum on September 8, 2013. Hamed says she is prepared to be flogged to defend the right to leave her hair uncovered in defiance of a “Taliban”-like law. She faces a possible whipping if […]

Amira Osman Hamed wadda ake tuhuma da laifin kin lullubi a kasar SudanWata ’yar Sudan za ta fuskanci hukuncin bulala a kotu, bayan da ake ta tafka shari’a kan keta dokar sutura ta kamala da Gwamnatin Sudan ta kafa tun a shekarar 1989, bayan da aka sameta da laifin rashin lullube kanta.

Tun a cikin watan Satumbar bana aka fara shari’ar Amira Osman Hamid, inda lauyyanta ya bukaci a janye tuhumar, amma tunda an gurfanar da ita a gaban kotu, ana auna yadda ya kamata a ci gaba da wannan shari’a, kamar yadda lauyan Amira suka bayyana a Jebel Aulia da ke wajen birnin Khartoum.
Kotu na jiran mai gabatar da kara, inda yake da zabin dawo da karar tuhumarta a gaban kotu, don a kara saurarenta, ko kuma ya yi watsi da ita, kamar yadda Amira ta bayyana.
Ba a sanya ranar da sake sauraren karar ba, amma daya daga cikin lauyoyinta, Kamal Omar, ya bayyana cewa, “wannan ba yana nufin an kammala shari’ar ba ne.”
A karkashuin dokar Sudan, ana bukatar mata su lullube kawunansu da hijab, amma Amira ta ki, inda ta bayyana cewa hukumomi na son ganinsu tamkar matan ’yan Taliban.
Wannan shari’a tata ta samu goyon bayan kungiyoyin fafutikar hakkokin dan Adam. Ta ce an fara tuhumarta ne bayan da wani dan sanda ya umarceta da ta lullube kanta, a lokacin da ta ziyarci wani ofishin gwmnati da ke Jebel Aulia a cikin watan Agustan bana.
An dai taba kwata irin wannan shari’a a shekarar 2009, inda wata ‘yar jarida, mai suna Lubna Ahmad Al-Hussain, wadda a sanadiyyarta kungiyoyin duniya suka yi ta kwakwazon kwatar hakokin matan Sudan. Lubna ta sanya tufafi masu shara-shara a bainar jama’a, dona haka aka ci tararta, amma ta ki biya. An tsareta na tsawon kwana daya, ammma sauran matan da aka kama su tare a wani wurin cin abinci, duk an zane su da bulala.