Ana ta zuba kudin cacar ranar haihuwar jaririn gidan sarautar Birtaniya

An fara karbar kudin caca, don cankar ranar da Gimbiya Kate za ta haifi jaririn gidan sarautarBirtaniya. An yi hasashen haihuwar jaririn a tsakiyar watan Yulin bana. Kuma iyayen jaririn sun ce ba su da masaniya kan jinsin jaririnsu.Jami’in Caca Paddy Power, ya fito da lambobin mara, wadanda za a canka a amkon farko na […]

Ana ta zuba kudin cacar ranar haihuwar jaririn gidan sarautar Birtaniya
Ana ta zuba kudin cacar ranar haihuwar jaririn gidan sarautar Birtaniya

An fara karbar kudin caca, don cankar ranar da Gimbiya Kate za ta haifi jaririn gidan sarautarBirtaniya. An yi hasashen haihuwar jaririn a tsakiyar watan Yulin bana. Kuma iyayen jaririn sun ce ba su da masaniya kan jinsin jaririnsu.
Jami’in Caca Paddy Power, ya fito da lambobin mara, wadanda za a canka a amkon farko na watan Yulin. Su kuwa ’yan caca sai zuba kudi suke, inda suke ganin cacar da za a buga da dimbin kudin da za a watsar sai sun fi na lokacin da Gimbiya Diana za ta haihu.
A shekarar 1982, Gimbiya Diana, wadda ta mutu a shekarar 1997, ta ja hankalin al’umma, in da ta bayyana cewa za a haifi Yarima Williams a ranar 1 ga Yuli, amma sai aka haife shi kwanaki 10 kafin ranar.

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda