Ana takaddama kan tayar da sansanonin ’yan gudun hijira
Wadansu ’yan gudun hijirar da suka fito daga karamar Hukumar Gwoza sun sa kafa sun shure umarnin da gwamnatin Jihar Borno ta bayar na cewa za ta tayar da sansanonin ’yan gudun hijira da suke makarantun firamare da sakandaren garin Maiduguri, saboda daliban makarantun su fara karatu a yanzu. A bisa tsarin gwamnatin ’yan gudun […]
Wadansu ’yan gudun hijirar da suka fito daga karamar Hukumar Gwoza sun sa kafa sun shure umarnin da gwamnatin Jihar Borno ta bayar na cewa za ta tayar da sansanonin ’yan gudun hijira da suke makarantun firamare da sakandaren garin Maiduguri, saboda daliban makarantun su fara karatu a yanzu.
A bisa tsarin gwamnatin ’yan gudun hijirar za su bar makarantun ne zuwa wasu wuraren da aka tanadar musu, don a bai wa dalibai dama su ci gaba da karatunsu bayan da suka kwashe tsawon lokaci suna zaman dirshan a gida.
Gwamnati ta ce ta tanadar wa ’yan gudun hijirar da suka fito daga Gwoza wadanda suke gudun hijira a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da Kwalejin Arabiyya, zuwa sansanin gudun hijra na Bakasi, sai dai wadansu daga cikin ’yan gudun hijirar sun kekasa kasa sun ce ba za su koma sansanin na Bakasi da ke wajen gari ba, saboda zargin rashin tsaro.
Malam Ali Gwoza, daya daga cikin wadanda suka ce ba za su koma sansanin na Bakasi ba, ya shaida wa wakilinmu cewa tafi gara su koma garin Gwoza, “Mu ’yan gudun hijirar da muke zaune a wadannan wurare ba za mu koma Bakasi ba saboda Bakasi wajen gari ne, babu cikakken tsaro. Kowa ya san Bakasi babu tsaro kuma mun fi jin dadin nan da yake cikin gari ne akwai cikakken tsaro, amma wancan wurin babu tsaro, da mu koma can gara mu koma garin Gwoza ya fi mana kwanciyar hankali, domin an ce an karbi Gwoza. An ce wai ’yan makaranta ne za su koma, to ai mun yarda cewa za a bude makaranta domin
Karatu yana da kyau ga ’ya’yanmu da kannenmu. To amma idan muka tashi, za mu koma Gwoza ne, ba mu yarda da wancan wuri ba, saboda babu tsaro.”
Shi kuwa Malam Bala Tanko, cewa ya yi “Dukkan mutanen Gwoza mun amince ba za mu koma Bakasi ba, domin babu tsaro, kuma kowa ya san wurin bayan gari ne saboda haka sai dai mu koma Gwoza. Ko jiya Sarkin Gwoza ya zo ya ce tilas mu koma Bakasi, mu kuma ba ma son wurin domin ba cikakken tsaro, saboda haka ba za mu bi umarnin na gwamnati ba, duk da cewa bude makarantun na da kyau amma idan muka tashi to za mu tafi Gwoza ne.”
Tun da farko sai da Sarkin Gwoza Mai martaba Alhaji Muhammadu Idrisa Timta, ya kai ziyara sansanonin don shaida wa jama’arsa kudirin gwamnati na tayar da su daga sansanonin zuwa sansanin na Bakasi, amma sai ya samu turjiya daga ’yan gudun hijirar na masarautarsa ta Gwoza.