Ana takun saka tsakanin China da Amurka

Amurka ta kakaba wasu sababbin takunkumi na Dalar Amurka biliyan 200 a kan kayayyakin China a yayin da take fadada yakin da take yi da kasar kan cinikayya. kari mafi yawa zai shafi haraji a kan kayayyaki fiye da 5,000, wanda shi ne mafi girman takunkumi kawo yanzu. Kayan da karin ya shafa sun hada […]

Ana takun saka tsakanin China da Amurka
Ana takun saka tsakanin China da Amurka

Amurka ta kakaba wasu sababbin takunkumi na Dalar Amurka biliyan 200 a kan kayayyakin China a yayin da take fadada yakin da take yi da kasar kan cinikayya.

kari mafi yawa zai shafi haraji a kan kayayyaki fiye da 5,000, wanda shi ne mafi girman takunkumi kawo yanzu.

Kayan da karin ya shafa sun hada da jakunkunan hannu da shinkafa da yadudduka, amma an cire agogogunan zamani da kayan rubutu.

Sai dai China ta sha alwashin mayar da martani idan har Amurka ta dauki wannan mataki.

Sababbin harajin za su fara aiki daga 24 ga wannan wata na Satumba, inda za su fara da kashi 10 cikin 100, kana su tashi zuwa kashi 25 cikin 100 a farkon badi.

Shugaba  Donald Trump ya ce wannan jerin takunkumin sun biyo bayan halayyar China ce ta “Rashin adalci a cinikayya, da suka hada da bai wa kamfanonin kasar tallafi a wasu sassa na kasar Amurka,” inji shi.

Sai dai yawancin kamfanonin Amurka ba su goyi bayan wannan matakin na Shugaba Trump ba.

Manoma da masana’antu masu kere-kere da manyan kamfanoni sun shiga wata hadaka da ke adawa da karin harajin, domin sun ce suna karewa ne a kan  mutanen Amurka.

A nata bangaren kuma, China ta kakaba wa Amurka takunkumi na Dalar Amurka biiyan 50 a baya, a fannin kayan noma, wanda shi ne ya fi damun magoya bayan Shugaban na Amurka.

Gwamnatin China ta kuma shirya saka wa wasu kayayyakin Amurka harajin Dala biliyan 60, sannan tana da shirin fadada shi kamar yadda BBC ya ruwaito.