Ana tallata mukamin minista a Iraki

A wani al’amari mai ban mamaki, sabuwar gwamnatin Iraki ta Bullo da wani sabon tsari na ba mutanen da ke sha’awar zama minista a kasar su aiko da sha’awar haka, bayan gwamnatin ta tallata mukaman ta Intanet. Gwamnatin kasar ta ce ta samu bayanan dubban  mutanen da suka aiko da bukatar neman mukaman minista a […]

Ana tallata mukamin minista a Iraki

A wani al’amari mai ban mamaki, sabuwar gwamnatin Iraki ta Bullo da wani sabon tsari na ba mutanen da ke sha’awar zama minista a kasar su aiko da sha’awar haka, bayan gwamnatin ta tallata mukaman ta Intanet.

Gwamnatin kasar ta ce ta samu bayanan dubban  mutanen da suka aiko da bukatar neman mukaman minista a Intanet

Wanda aka zaBa domin zama Firayi Ministan kasar, Abdel Abdul Mahdi ne ya Bullo da sabon tsarin kamar yadda BBC ya ruwaito.

Ya wallafa bukatar ce a shafin Facebook inda ya ce waDanda ke da kwarewa suna iya aikewa da sunayensu da bukatarsu zuwa shafin Intanet na gwamnatin kasar.

Manufarsa ita ce samun mutanen da ke da kwarewa sosai a fannoni da dama domin ba su mukaman minista kuma waDanda ba su da alaka da wani Bangare na siyasa ko akida da ya jefa kasar cikin rikici tun kawar da gwamnatin Saddam Hussien a shekarar 2003.

Babban kalubalen da ke gaban sabuwar gwamnatin shi ne sake gina Iraki bayan shafe shekara huDu kasar na fama da yaki da mayakan IS, rikicin da ya lakume rayukan dubban mutane tare da raba miliyoyi da gidajensu.

Gwamnatin ta ce sama mutum dubu 36 da 6 da suka aiko da bukatunsu na neman mukaman  ministoci a Intanet, kuma a cewar gwamnatin yawancinsu ba su da alaka da wata jam’iyyar siyasa, kashi 15 daga cikinsu mata ne daga sassan Iraki.