Ana tilasta wa Musulmi yin ridda a Afirka ta Tsakiya – Amnesty

kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta duniya wato Amnesty International ta ce ana tilasta wa Musulmi yin ridda a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a matsayin sharadin barinsu su zauna a kasar.Wata jami’ar kungiyar Amnesty International mai hedkwata a Landan, Misis Joanne Marines, ta ce mayakan kungiyar anti-Balaka da suka tilasta wa dubban Musulmi barin kasar […]

Ana tilasta wa Musulmi yin ridda a Afirka ta Tsakiya – Amnesty
Ana tilasta wa Musulmi yin ridda a Afirka ta Tsakiya – Amnesty

kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta duniya wato Amnesty International ta ce ana tilasta wa Musulmi yin ridda a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a matsayin sharadin barinsu su zauna a kasar.
Wata jami’ar kungiyar Amnesty International mai hedkwata a Landan, Misis Joanne Marines, ta ce mayakan kungiyar anti-Balaka da suka tilasta wa dubban Musulmi barin kasar a bara, yanzu sukan gindaya sharudda ne ga duk Musulmin da ke komawa kasar, cewa muddin suna son zama to, su yi watsi da addininsu.
Rahoton na Amnesty da aka wallafa a ranar 31 ga Yuli mai taken: “Shafe Jinsi: Musulmi na fuskantar shafewa daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya,” Amnesty ta kara da cewa, Musulmin Afirka ta Tsakiya na fuskantar bakin zalunci inda ake tilasta su shiga addinin Kirista ko a hallaka su.
Rahoton ya kara da cewa, “mayakan anti-Balaka suna hana Musulmi gudanar da addini a bainar jama’a tare da tilasta su shiga addinin Kirista ko a kashe su.”  kungiyar ta ce, mayakan anti-Balaka suna amfani da rashin gwamnati a kasar inda suka kaddamar da shirin shafe al’umma Musulmi a kasar.
Joanne Mariner, wadda babbar mai ba da shawara ce kan magance rigingimu na kungiyar ta shaida wa gidan talabijin na Aljazeera bayan fitowar rahoton cewa Musulmin da suke rabin yammacin kasar an musguna musu tare da tilasta su ridda daga addininsu.
Akwai fiye da Musulmi dubu 30 da suke zaune a wasu yankuna bakwai da sojojin Majalisar dinkin Duniya ke gadinsu a sassan kasar, kuma suke zaune a kebe, galibi a yankunan karkara cikin kunci, inji rahoton.
“Ba su barinsu su ma nuna su Musulmi ne; idan suna wajen yankunansu ba za a bari su yi Sallah ba, ba za su sanya suturar da za ta nuna su Musulmi ne ba,” inji Mariner. Ta kara da cewa “dorewar rayuwarsu ta dogara ne kan kulla yarjejeniya a kullum da mayakan anti-Balaka.”
Amnesty ta ce, hatta a wuraren da sojojin Majalisar dinkin Duniya suke ana musguna wa Musulmin.
Rahoton Majalisar dinkin Duniya ma ya ce:  “Mayakan anti-Balaka sun kai hare-harea gidajen Musulmi, sun kashe yara da mata tare da sacewa ko lalata dukiyarsu.”
Wata Jakadiyar Amurka ta ce, an ruguza kusan daukacin masallatai 436 da ke Afirka ta Tsakiya lokacin rikicin. Samantha Power, Jakadiyar Amurka a Majalisar dinkin Duniya ta yi kiran a nemo mafita kan “wannan danyen hukunci.”
Saboda haka kungiyar ta Amnesty ta roki gwamnatin kasar da Majalisar dinkin Duniya da manyan kasashen su sa baki domin gudun dada kazancewar lamarin.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50