Ana tsananin buƙatar man fetur saboda ayyukan asibitoci a Gaza — MDD

Isra’ila ta amince da barin manyan motoci 20 ɗauke da kayan agaji sun shiga Gaza.

Ana tsananin buƙatar man fetur saboda ayyukan asibitoci a Gaza — MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa kan yadda ake tsananin buƙatar man fetur saboda gudanar da ayyukan asibitoci da samar da ruwan sha a Gaza.

MDD ta yi koken ne yayin da manyan tankokin mai ke tunkarar kan iyakar Masar da Gaza, wanda ta ce har yanzu ba a shigar da mai cikin Gaza ba.

Ofishin Kula da Ayyukan Jinkai na MDD ya ce ya zama wajibi a buƙaci man, kuma rashinsa ka iya kawo rashin tsaftataccen ruwan sha a Gaza, saboda cibiyoyin bayar da ruwan sha da famfuna ba za su yi aiki ba idan babu man fetur.

Yayin da tankokin ke ci gaba da jiran izinin shiga Gaza bari mu duba dalilan da ya sa ake buƙatar man a Gaza, da wuraren da ke buƙatarsa.

Haka kuma ana buƙatar man domin kunna injunan bayar da wutar lantarki a asibitocin yankin.

A makon da ya gabata ne ƙungiyar agaji ta Red Cross ta yi gargaɗin cewa asibitocin Gaza na cikin hatsarin komawa ‘mutuware’ (Dakin ajiye gawarwaki) idan ba su samu wutar lantarki ba.

Cibiyoyin lafiya na cikin mawuyacin halin tun bayan ta Isra’ila ta ƙaddamar da hare-hare kan Gaza, yayin da take yi wa yankin luguden wuta ta sama da makaman atilare.

A wani mataki na mayar da martani kan mayaƙan Hamas waɗanda suka kai hari Isra’ila mako biyu da suka gabata tare da kashe mutum 1,400.

Isra’ila ta ce ba za ta mayar da wutar lantarki zuwa Gaza ba, har sai Hamas ta sako mutanenta fiye da 200 da tayi garkuwa da su a lokacin harin.

To amma a jiya Isra’ila ta amince da barin manyan motoci 20 ɗauke da kayan agaji sun shiga Gaza bayan shafe kwanaki ana tattaunawa.

Rufe ‘boda’ ya kawo yunwa da rashin aiki a Arewa —CNG

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024