Ana tsine min a masallatai saboda #EndSARS —Aisha Yesufu
Ta yi mamakin ana tsine mata yanzu alhali ta yi irinsa a zamanin Jonathan ba a kushe ba
Aisha Yesufu mai fafutikar kare hakkin dan Adam ta koka bisa tsinuwar da ta ce ana mata a masallatai bayan an idar da sallah.
Ta yi mamakin irin tofin Allah tsine da ake mata saboda fafukikar da take yi, duk da cewa ta yi hakan a lokacin mulkin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ba tare da an yi tir da ita ba.
- #EndSARS: A gaggauta kamo Nnamdi Kanu —Bayari
- Buhari ya ba ministoci mako daya su kawo rahoton rikicin #EndSARS
“Na samu labarin cewa ana ta tsine min a masallatai!
“Mutane na ware lokacin idan sun idar da Sallah suna addu’ar tsinuwa a kaina.
“Ina tambayan su sau nawa suka tsine min a lokacin da nake irini wannan fafutika a lokacin Janathan?
Mai fafutikar ta wallafa hakan ne a shafinta na Twitter a ranar Juma’a 30 ga watan Oktoba, 2020.
Tun bayan da Aisha Yesufu ta bukaci matasan Arewa su fito su shiga zanga-zangar #EndSARS mutane da dama ciki har da jaruman masana’antat fim ta Kannywood da wasu daidaikun mutane suka yi tir da kiran nata har wasunsu suka yi bidiyo suna mayar mata da martani.
Aisha Yesufu na daga cikin wadanda suka assasa fafutikar #BringBackOurGirls na neman ganin an dawo da ‘yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace.
Daga baya tafiyar ta yi ta fadada tare da shiga sauran na’ukan gwagwarmayan kwato ‘yancin dan Adam, musamman mata.