Ana tsuga wa kamfanonin jiragen sama haraji – Shugaban IRS

Manajan Daraktan Kamfanin Sufurin Jiragen Sama na IRS, Alhaji Rabi’u Isyaku Rabi’u ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta gaggauta sake fasalin harajin da take karba daga kamfanonin sufurin jiragen sama, inda ya ce ana tsuga wa kamfanonin sufurin jiragen sama haraji. Ya yi bayanin ne lokacin da yake kaddamar da hada-hadar sufurin jiragen sama na Air […]

Ana tsuga wa kamfanonin jiragen sama haraji – Shugaban IRS

Manajan Daraktan Kamfanin Sufurin Jiragen Sama na IRS, Alhaji Rabi’u Isyaku Rabi’u ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta gaggauta sake fasalin harajin da take karba daga kamfanonin sufurin jiragen sama, inda ya ce ana tsuga wa kamfanonin sufurin jiragen sama haraji.

Ya yi bayanin ne lokacin da yake kaddamar da hada-hadar sufurin jiragen sama na Air Peace a tsakan Legas zuwa Kano, inda ya ce kamfanonin jiragen saman Najeriya suna hada-hadarsu ne a mummunan yanayi. Alhaji Rabi’u ya ce: “Kamfanonin jiragen saman Najeriya na fama da dimbin haraji; muna bayar da haraji mai yawa, tare da dimbin kudin da muke kashewa, farashin mai ba ya tabbas, akwai harajin hada-hadar ayyuka (bAT) da na Hukumar Sufurin Sama (NCAA) da na Hukumar Sararin Samaniya ta Najeriya (NAMA) da na Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN), kodayake suna tallafa wa kansu, amma kamfanonin jiragenmu na bukatar a tallafa musu, ta yadda za mu samu karuwa daga fasinjojin Najeriya da muke dauka.

“Kun ga yadda kamfanin jiragen saman Med-biew ke ta fafutika,suna bukatar tallafi, ga kamfanin Air Peace zai fara sufuri a tsakanin kasashen duniya. Wannan wani ci gaba ne da ake maraba da shi; Azman na kokarin kwatanta irin haka. Don haka idan muka samu tallafi daga gwamnati, yanayin zai zama mai alfanu ga kowa.

“Za mu tara dimbin kudaden musayar kasashen waje, wadanda muke biyan kamfanonin jiragen saman kasashen waje. Za mu bunkasa mu samar da aikin yi a fannin sufurin jiragen sama a Najeriya tare da bunkasa tattalin arzikinmu,” inji shi.

Dangane da kasuwar Afirka guda ta hada-hadar sufurin jiragen sama (SAT), ya ce: “Masu hada-hadar sufurin jiragen sama a Najeriya suna kokawa, amma wannan wani abu da aka dade da yin sa tsawon lokacin da ya gabata; tun lokacin sda aka yi yarjejeniyar Yamoussoukro. Abin da kawai nake son cewa shi ne mu yi kokarin aiki tukuru, mu kara kutsawa kasuwar hada-hada don gwamnatinmu ta ba mu tallafin da muke bukata.”

 

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno