Ana tuhumar dan Gwamna Sule Lamido da kisan wani yaro
A ranar Talatar da ta gabata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Nomansland ta ci gaba da sauraren shari’ar da ake yi tsakanin iyayen wani yaro da kuma dan Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Aminu Sule Lamido bisa zargin kisan wani yaro, sakamakon buge shi da mota da ya yi a unguwar Sabuwar kofa cikin Jihar […]
A ranar Talatar da ta gabata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Nomansland ta ci gaba da sauraren shari’ar da ake yi tsakanin iyayen wani yaro da kuma dan Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Aminu Sule Lamido bisa zargin kisan wani yaro, sakamakon buge shi da mota da ya yi a unguwar Sabuwar kofa cikin Jihar Kano a bara.
A lokacin gudanar da shari’ar, iyayen yaron mai suna Nasiru Sabo sun zargi Aminu Sule Lamido da kin biyan Naira miliyan 35 a matsayin diyyar ran dansu kamar yadda kotun baya ta bukata.
Lauyan da ke kare wanda ake kara, Barista Isa Ahmad ya shaida wa kotu cewa sun gaza biyan diyyar ne sakamakon shigowar wasu mutane cikin shari’ar. “Mu a iya saninmu mutum daya ne, to ba mu san yadda aka yi aka kara wasu mutane uku a cikin shari’ar ba. Ba mu san daga inda suke
Ba,” inji shi.
Har ila yau lauyan ya nemi kotun da ta kara musu lokaci, inda za su zauna da iyayen yaron don yin sulhu a tsakaninsu, bukatar da kotun ta amince da ita.
Alkalin kotun, Mai shari’a Faruk Ahmed ya dage shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Disamba don ci gaba da sauraren shari’ar.