Ana tuhumar daurarren mai unguwa da cinye filin marayu
A daidai lokacin da Mai unguwar Dabai Alhaji Jamilu Garba ke zaman kurkuku bisa samunsa da laifin sayar da filayen bogi ga wani mazaunin unguwarsa da kotun Shari’ar Musulunci ta kofar Kudu ta yi, sai kuma ga wasu marayu sun shigar da kara gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge Waje inda suke kukan ya […]
A daidai lokacin da Mai unguwar Dabai Alhaji Jamilu Garba ke zaman kurkuku bisa samunsa da laifin sayar da filayen bogi ga wani mazaunin unguwarsa da kotun Shari’ar Musulunci ta kofar Kudu ta yi, sai kuma ga wasu marayu sun shigar da kara gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge Waje inda suke kukan ya cinye musu filin da mahaifinsu ya bar musu gado.
Idan za a iya tunawa a watan jiya ne wani mutum mai suna Rabi’u Idris ya kai karar Alhaji Jamilu Garba da wani mai suna Abubakar Iliyasu gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta kofar Kudu cewa sun hada baki sun sayar masa da wasu filaye guda biyar a unguwar a kan Naira miliyan biyu da dubu 25 wanda daga baya ya gano filayen ba nasu ba ne.
Bayan ya amsa laifinsa ne alkalin kotun Mai shari’a Ibrahim Sani Sarki Yola ya yanke wa mai unguwar hukuncin daurin wata tara ba zabin biyan tara. Sannan ya yanke masa daurin wata shida ko biyan tarar Naira dubu 10 kan wani laifin. Mai unguwar yana kurkuku ne marayun suka shigar da kara inda suka shaida wa kotun ta Fagge Waje cewa mai unguwar ya cinye musu filinsu na gado.
Lokacin da aka karanta masa laifin da ake zarginsa mai unguwar ya amsa laifinsa inda ya nemi kotun da ta yi masa sassauci.
Alkalin Kotun Mai shari’a Abbas Magashi ya umarci mai unguwar ya biya Naira dubu 150 kudin filin marayun.