Ana tuhumar Fulani 18 da laifin kisa a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka
Akalla Fulani makiyaya 18 ake zargin da laifin kisan wasu mutane a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka kwanakin baya. Hakan ya faru ne a wasu hare-hare guda biyu da suka kai garuruwan Gamboula da kuma Nola masu iyaka da Kamaru. Wata majiya ta tabbatar da cewa hare-haren an kai su ne a cikin dare a lokacin da […]
Akalla Fulani makiyaya 18 ake zargin da laifin kisan wasu mutane a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka kwanakin baya. Hakan ya faru ne a wasu hare-hare guda biyu da suka kai garuruwan Gamboula da kuma Nola masu iyaka da Kamaru.
Wata majiya ta tabbatar da cewa hare-haren an kai su ne a cikin dare a lokacin da mutane suke runtsawa. Saboda haka mutane suka tashi a firgice. Hakan kuma ya kaiga mutane sama da 10 suka ji rauni sakamakon hargitsin da ya biyo baya. Hakan kuma ya sake sa jama’a rayuwa a cikin fargaba.
Tuni kuma wasu jama’a suka fara kauracewa zuwa garuruwan Carnot da kuma Berberati. Wasu bayanai daga majiyoyi da dama na cewa al’amurra sun dagule a garin Gamboula, inda mayakan sa-kai na anti-Balaka wadanda akasarin su Kiristoci ne suka fito suka dauki makamai domin daukar fansa akan Fulani wadanda akasarinsu Musulmi ne. Irin wadannan makamatan hare-hare sun faru a karshen makon jiya ne, a garin Bambari da yake tsakiyar kasar.
Akan irin wannan halin ne kuma Hukumar Majalisar dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijira ta yi kira da a kai wa Fulani makiyaya dauki da gaggawa sanadiyyar ukubar da suke sha a yanzu haka sakamakon kisar da ake tuhumarsu da aiwatarwa. Sama da Fulani 400 akasari mata da kananan yara suke cikin wani hali na ni-’yasu a garin Yaloke da yake arewa da babban birni Bangui.
Tun a watan Maris na shekarar2013, lokacin da ’yan tawayen Seleka suka kwace mulki a hannun Shugaba Francois Bozize, ya zo kuma daga bisani aka tilasa musu sauka akan kujerar mulki.
Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ta fada cikin wani hali na dagulewar al’amura, kisan rayukan jama’a, kona gidaje, barnatar da dukiyoyi, da kuma tilasa wa jama’a kaurace wa muhallansu. Duk da aikin dakarun wasu kasashe hadi da na kungiyoyi daban-daban kamar Sngaris na kasar Faransa, MINUSCA na Majalisar dinkin Duniya da kuma Eufor-RCA na kungiyar hadin kan turai, amma duk da haka kuma al’amurra suka kasa daidaituwa.