Ana tuhumar koci da laifin yin fyade a Uganda
Rundunar ’yan sandan Uganda ta samu nasarar kama wani koci mai suna Peter Wemali da laifin yin fyade ga wasu mata uku da yake horar da su yadda ake gudu. Ita dai Uganda tana kokarin ganin ta shiga gaban kasashen Kenya da na Habasha ne a gasar tsere al’amarin da ya sa ta fi mayar […]
Rundunar ’yan sandan Uganda ta samu nasarar kama wani koci mai suna Peter Wemali da laifin yin fyade ga wasu mata uku da yake horar da su yadda ake gudu.
Ita dai Uganda tana kokarin ganin ta shiga gaban kasashen Kenya da na Habasha ne a gasar tsere al’amarin da ya sa ta fi mayar da hankali wajen horar da matasa maza da mata don su rika fafatawa a gasar tsere a ciki da wajen kasar.
Hakan ta sa kasar ta yanke shawarar daukar kwararren mai horar da ’yan tsere mai suna Peter Wemali amma abin bakin ciki sai ya yi amfani da wannan dama wajen yi wa akalla uku daga cikin ’yan matan da yake horarwa fyade.
Rahoton da kafar sadarwar Daily Monitor ta kalato ya nuna Peter Wemail ya yi wa wasu ’yan mata da shekarunsu suka kama 15 da 16 da kuma 17 fyade a lokuta daban-daban a shekarar 2013 da kuma 2014.
Jami’in dan sanda mai kula da yankin Sipi da ke Gabashin kasar inda al’amarin ya faru mai suna James Ruhbeza ya tabbatar da cewa yanzu haka kocin ya shiga komarsu kuma suna nan suna gudanar da bincike don ganin an zartar masa da hukuncin da ya dace da shi.
Asirin kocin ya tonu ne bayan shahararren dan tseren kasar Moses Kipsiro wanda ya samu nasarar lashe lambar Zinare a gasar tsere ta kasashe renon Ingila ya sanar da hukumomin kasar halin da ake ciki bayan ’yan matan da aka yi wa fyaden sun shaida masa halin da suke ciki.
Baya ga wadannan mata uku da kocin ya yi wa fyade, an samu labarin ya sake yi wa wata yarinya fyade a sansanin horarwa a bara.