Ana tuhumar limaman coci da kashe mace domin tsafi
dimbin mutanen garin Abgado da ke Jihar Ogun ne suka yi dafifi don tarbar Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Ahmad Iliyasu lokacin da ya isa garin a ranar Larabar makon jiya don gane wa idonsa mafakar wadansu mutane da ake zargi da yin tsafi da sassan jikin mutane bayan samun labarin kisan wata mace, wacce ake […]

dimbin mutanen garin Abgado da ke Jihar Ogun ne suka yi dafifi don tarbar Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Ahmad Iliyasu lokacin da ya isa garin a ranar Larabar makon jiya don gane wa idonsa mafakar wadansu mutane da ake zargi da yin tsafi da sassan jikin mutane bayan samun labarin kisan wata mace, wacce ake zargin wasu limaman coci ne suka yi.
A zantawarsa da Aminiya, Kwamishinan ’Yan sandan ya ce a ranar 10 ga watan jiya ne babban basaraken yankin Abgado ya shaida wa ofishin ’yan sandan yankin cewa an gano gawar mace a wani kango, wacce aka cire wa kai da kafafu da hannuwa. “Nan take na umarci Babban Jami’in ’Yan sandan yankin, CSP Olatunji Omonijo ya gudanar da bincike ya kuma kawar da gawar matar da ba a gano ko wace ce ba. Bayan binciken da muka gudanar, mun samu nasarar kama mutum uku da suka hada da limaman coci biyu da wanda ya ba su hayar gidan da suke ciki,” inji shi.
daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Akindele ya shaida wa Aminiya cewa shi limamin coci ne kuma matar farkarsa ce da suka dade suna tare kimanin shekara biyu. Ya ce a ranar da lamarin zai faru, matar mai suna Iya Ahnu ta ziyarce shi. “A lokacin da ta zo ta same ni ranta a bace, ta ce in ba ta Naira dubu goma domin ta kara jari a kasuwancinta. Sai na ce mata ta yi hakuri zan ba ta ba da jimawa ba. Bayan ta kishingida tana hutawa sai na buga mata katago a kai, daga bisani na cire kanta da hannuwanta da kafafunta,” inji shi.
Wadanda ake zargin sun binne sassan da suka cire a jikin matar a daura da Cocin Judah, wanda ke Lamba 13 a Unguwar Robiyan da ke yankin Abgado, cocin da yake mallakar daya daga cikin wadanda ake zargin ne mai suna Ayodele Bamiduro, kamar yadda Kwamishina Ahmad Iliyasu ya fadilokacin da ya jagoranci ’yan jarida zuwa cocin, bayan ya kai su kangon da wadanda ake zargin suka jefar da gawar.
A lokacin ziyarar gani da idon, wakilin Aminiya ya ga gawar matar kuma ya ga kayayyakin da suka shafi na tsubbace-tsubbace da riguna da wandunan mutane da aka tara su a gefe guda a wani daki a gidan wadanda ake zargin. A cikin cocin da ake zargin an binne wasu sassan jikin matar, akwai hoto mai alamar Yesu da ganguna da wasu kayayyaki da ake amfani da su a coci.
Da yake yi wa dandazon jama’ar yankin da suka taru don gane wa idanunsu al’amarin, Kwamishinan ya yi kira gare su da su zamo masu taka-tsantsan da irin mutanen da suke mu’amala da su. Ya ce duk lokacin da wani ko wata ya shirya kai wa wani ziyara to ya sanar da ’yan uwansa ko abokan zamansa. Ya ce da zarar sun kammala bincike, za su gurfanar da wadanda ake zargin kuma za su ci gaba da dakile ayyukan batagari.
Ko a ’yan watannin da suka shude ’yan sanda sun yi nasarar kama wadansu limaman coci da ake zargi da kisan wata mace, inda suka binne wasu sassan jikinta a wani coci da ke daura da garin Iwekoro da ke kusa da garin Abgado.