Ana tuhumar ma’aikacin kotu kan zambar Naira miliyan biyu

An gurfanar da wani ma’aikacin Kotun daukaka kara ta Shari’ar Musulunci mai suna dalhatu Yahaya, da ke zaune a Unguwar Arawa a gaban kotun Yankin ta Doma da ke garin Gombe bisa zargin zamba cikin aminci na sama da Naira miliyan biyu.Ana tuhumar dalhatu Yahaya ne da laifin karbar kimanin Naira miliyan biyu da dubu […]

Ana tuhumar ma’aikacin kotu kan zambar Naira miliyan biyu
Ana tuhumar ma’aikacin kotu kan zambar Naira miliyan biyu

An gurfanar da wani ma’aikacin Kotun daukaka kara ta Shari’ar Musulunci mai suna dalhatu Yahaya, da ke zaune a Unguwar Arawa a gaban kotun Yankin ta Doma da ke garin Gombe bisa zargin zamba cikin aminci na sama da Naira miliyan biyu.
Ana tuhumar dalhatu Yahaya ne da laifin karbar kimanin Naira miliyan biyu da dubu tamanin daga wurin wani mai suna Mustapha Muhammad, mazaunin Unguwar Hammadu Kafi, bisa yarjejeniyar zai ba shi ribar Naira dubu 165 bayan wata daya.
dan sanda mai gabatar da kara Kofur Sama’ila Shu’aibu, ya shaida wa kotun cewa dalhatu Yahaya, ya karbi kudin ne a ranar 5 ga Afirilun shekara ta 2013 inda ya ce zai ba Mustaphan ribar Naira dubu 165 bayan ya yi amfanin da kudin wajen sayen kwamfutoci laptops, ya raba wa ma’aikatansu bashi, inda ya kasa cika alkawari kuma yake gudunsa har tsawon wata shida kafin a kama shi, ya ce aikata hakan laifi ne da ya saba wa sassa na 311 da 320 na kundin Penal Code.
Da kotu ta juya ga wanda ake tuhumar ya musanta zargin, inda mai gabatar da karar ya nemi kotun da ta ba su rana don gabatar da shaidunsu.
Alkalin kotun Mai shari’a Alhaji Bashir Bappah, ya ba da belin wanda ake tuhumar bisa sharadin wanda zai dauki belin ya kasance sanannen mutum ne kuma zai ajiye Naira dubu 500 da fasfo da cikakken adireshinsa da kuma lambar waya.